Manchester City ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Bayern Munich a wasan daf da na kusa da na karshe da suka fafata daren Laraba a Allianz Arena.
Erling Haaland ne ya ci kwallon daya tilon da ya baiwa City nasarar hada kwallo 4 – 1 jumulla a wasannin na gida da waje.Haaland ya barar da bugun finareti a mintuna na 37, kafin dan wasan na Norway ya huce haushinsa ya zura kwallo a mintuna na 57.
Da wannan nasara da kungiyar ta Ingila ta samu a wasan kusa da na karshe a Champions League karo na uku a jere za ta hadu da Real Madrid wanda kamar yadda suka yi a kakar wasanni da ta gabata a daidai wannan mataki, Madrid ce ta yi nasara a wancan lokaci, ko tarihi ya mamaita kansa?
Inter Milan
Ita ma Inter Milan ta kai zagayen daf da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da suka tashi 3-3 da Benfica, wato 5 – 3 jimilla.
Kungiyar Simone Inzaghi za ta kara da abokiyar hamayyarta na cikin gida AC Milan a wasan na hudun karshe, sakamakon kokarin kwallayen Nicolo Barella, Lautaro Martinez da Joaquin Correa.
Kungiyoyin biyu na Milan na kokarin zama kungiyar Serie A ta farko da ta lashe gasar manyan kungiyoyin Turai tun bayan da Inter ta dauki kofin a shekarar 2010.