Kungiyar agaji ta Nigerian Red Cross (NRC) da hadin gwiwar International Federation of Red Cross and Red Cressent (IFRC) ta horar da ’yan sa-kai 50 domin fadakar da mutane hanyoyin kare kai daga kamuwa da cutar amai da gudawa a Gombe.
Sakataren Yanki na kungiyar a Jihar Gombe, Murtala Aliyu, shi ne ya shaida wa wakilinmu hakan lokacin bayar da horon na kwana uku a Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke jihar.
- Dalilan da mata ke son miskilin namiji
- ’Yan sanda sun tada hargitsi a wurin tara sakamakon zaben Anambra
Murtala Aliyu, ya ce sun zabi su horar da ’yan sa-kan su 50 kan hanyar koya wa jama’a yadda ake hada ruwan gishiri da suga ne don bai wa wanda ya kamu da cutar amai da gudawa agajin gaggawa da idan suka samu horon za su shiga yankunan karkara su yi aiki na wata uku.
Ya ce sun zabi hada gishiri da suga ne saboda su taimaka wa gwamnati wajen shawo kan cutar ta hanyar wayar da kan al’umma.
A cewarsa, duk da cewa shirin horon ya samu tallafin kungiyar NRC da IFRC, amma suna neman tallafin gwamnati don fadada shirin.
Sakataren na Red Cross ya yi kira ga al’umma da su koyi tsaftar jiki da ta muhalli da shan ruwa mai tsafta don gudun kamuwa daga cutar kwalara.
Ya ce kasancewar a cikin su akwai ma’aikatan lafiya shi ya sa suka dauko su don taimakawa wajen tabbatuwar shirin.
Daga nan sai ya sake kira ga jama’a da su bai wa bangaren lafiya kulawa ta musamman don inganta rayuwarsu.
Wasu daga cikin mahalarta taron da muka zanta da su sun bayyana gamsuwarsu da shirin horon inda suka ce sun karu da ilimin da aka ba su.
Mahalarta taron an zabo su ne daga kananan hukumomin Balanga da Gombe.