Shugaban kungiyar ’yan Arewa mazauna jihohin Kudu maso Yamma, reshen Jihar Legas, Barista Abdulkadir Habib Maude ya karyata jita-jitar da wasu ke yadawa cewa kungiyar ta ruguje sakamakon rikicin shugabanci da ya kunno kai a tsakanin shugabanninta.
Barista Maude ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa, inda ya ce kungiyarsu na nan daram.
Ya ce, “kungiyarmu na nan daram, ba mu ruguje ba, kuma ba wanda muka kora daga kungiyarmu, sannan babu wani dan siyasa da muka taba karbar kudi a wurinsa, yanzu nake jin maganar daga bakinka. Wasu ne kawai suke so su kawo mana rudu su yi mana kama-karya. Shi ya sa muka ga ya dace mu mayar da hankali kan abin da zai kawo wa ’yan Arewa ci gaba a Jihar Legas da yankin Kudu maso Yamma na kasar nan. kungiyarmu ta samu ci gaba da bunkasa saboda jajircewar da muka yi. Saboda haka muna kira ga jama’a su ci gaba da ba mu goyon baya don cimma burin da muka sa a gaba na taimakon jama’a da bunkasar tattalin arziki da zaman lafiya”.
Shugaban ya yaba wa sarkin Sasa saboda shawarwari da goyon baya da yake ba kungiyar. “Dole mu yaba wa sarkin Sasa saboda taimakon da yake yi mana da sauran sarakuna da mutanen da suke ba mu goyon baya don ci gaban kungiyarmu”. Inji shi.
Daga bisani Barista Maude ya jaddada cewa kungiyarsu ba ta siyasa ba ce saboda haka kowane dan kungiya yana da ’yancin fadar albarkacin bakinsa bisa doka da oda, ba tare da wata matsala ba.
kungiyarmu na nan daram -Barista Maude
Shugaban kungiyar ’yan Arewa mazauna jihohin Kudu maso Yamma, reshen Jihar Legas, Barista Abdulkadir Habib Maude ya karyata jita-jitar da wasu ke yadawa cewa kungiyar…