Alhaji Umaru Shu’aibu wanda aka fi sani da danlami Kowanaka shi ne ya kafa kungiyar Hausa-Fulani a Jihar Nasarawa, wanda a yanzu yake uban kungiyar. Shi ne Sakataren kungiyar mahauta na kasa. A tattaunawarsa da ya yi da wakilinmu a Lafiya, ya ce kungiyarsu ba ta umurci ’yan kungiyarsu su zabi wani dan takara ba. Ya kuma tabo batun sace-sacen shanu da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:
Ka bayyana mana kadan daga cikin ayyukan kungiyarku na Hausa-Fulani?
kungiyar Hausa-Fulani kungiya ce da aka kafa ta don tabbatar da samun zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’umma. Wannan shi ne babban kira da kungiyarmu ke yi wa mambobinta a kullum, kuma kungiyar tana tabbatar da cewa kowa ya samu abin yi, wato tana wayar da kan mambobinta don su rike sana’a da muhimmanci. Tana kuma hana maula a tsakanin ’ya’yanta, wato ka tashi maimakon ka je sana’a sai ka rika tafiya ofis-ofis kana maula. Shi ya sa yau idan ka lura za ka ga mambobinmu daga masu yankan farce da masu aikin gyaran takalma da sayar da rake da turin baro da dai sauransu, babu wanda ke zaman banza domin ba ma goyon bayan haka.
Wadanne nasarori kungiyarku ta cimma a halin yanzu?
Alhamdullillah wannan kungiya a halin yanzu ta cimma nasarori da dama. Babbar nasarar da ta samu ita ce ta tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Hausa-Fulani da sauran al’ummomi a jihar nan. Yau duk inda ka shiga za ka ga mutanenmu suna zaune lafiya da sauran al’ummomi da Ubangiji ya hada mu daga nan Arewa har ma Kudu, inda mutanenmu sun yi kaka-gida wajen neman abincinsu. A kullum kuma muna kira ga iyaye su tura ’ya’yansu karatu domin shi ne babban gadon da za su iya bar musu. Muna gaya musu muhimmancin ilimin ’ya’yansu maza da mata. Akwai nasarori da dama da kungiyarmu ta cimma, kamar yadda na bayyana maka.
Ko kuna fuskantar wani kalubale a harkokin kungiyarku?
kalubalen da muke fuskanta a halin yanzu dai bai wuce na rayuwa ba, ma’ana halin da muka samu kanmu a ciki yau na tashin hankali. Domin a duk inda kake idan aka rika samun tashin hankali a wajen, hakan zai sanya ka a cikin damuwa, don abu ne da ba ka so ka gani. Idan ka lura wadannan wurare da ake tashin hankali akwai mutanenmu a wajen. Wasu ma rigingimun sun shafe su, saboda haka babu shakka ya kasance babban kalubale a gare mu shugabannin wannan kungiya, inda ya kamata a kullum mu rika gaya wa mutane cewa su rungumi zaman lafiya. Duk abin da aka yi maka na cutarwa kada ka ce dole sai ka rama, maimakon haka ka bar komai a wurin Allah, Zai dauka maka fansa. A halin yanzu muna iya kokari don tabbatar mun magance su kamar yadda na bayyana.
A ’yan kwanakin nan wasu ’yan kungiyarku sun sanar a kafafen yada labarai cewa za su zabi dan takarar gwamna na jam’iyyar APGA Mista Labaran Maku a zaben 2015. Me za ka ce a kan hakan?
Kamar yadda ka sani, duk abin da ya shafi harkar siyasa abu ne na ra’ayi da ba za ka hana wani yi ba. Sai dai abu ne na damuwa da takaici idan mutum ya ce ka fito ka yi magana da yawun kungiya ba tare da an umurce ka ka yi haka ba. Wannan babban kuskure ne. Bai kamata ka ari bakin mutane ka ci musu albasa ba, saboda haka ina so in yi amfani da wannan damar in sanar cewa wadannan mutane bada yawun kungiyarmu suka yi wannan magana ba. Ba mu umurce su ba. Watakila sun yi magana ne na ra’ayi irin nasu, wanda kamar yadda na bayyana ba za ka iya hana su ba. Amma mu dai kungiyarmu ba ta ma yarda cewa wadannan mutane Hausa-Fulani ba ne. In kuma Hausa Fulani ne, to ba mu san su ba. Idan kuma mun san su to ba su zauna da mu mun dauki wannan mataki a kungiyance ba.
Ina so in sanar cewa kungiyarmu ba ta siyasa ba ce. Akwai abubuwa da muka sa a gaba, wato muna neman ci gaban al’ummarmu ne a kodayaushe kamar yadda na bayyana maka a baya. Ni dai ina da nawa ra’ayi na jam’iyya da na ga ta dace in bi ta, kowa yana da irin wannan ra’ayi. Kowa ya sani cewa ina tareda gwamna Umaru Tanko Almakura na APC ne, kuma ina da dalilai da dama da suka sa nake goyon bayansa. Abu na farko shi ne na dade da zama a jihar nan, kuma duka gwamnonin da suka shude babu wanda ya gudanar da kyakkyawan mulki kamar na Almakura. Ya kawo mana ci gaba a kowane fanni na rayuwa a jihar nan, ko mahassada sun shaida hakan.