✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Lemo a Nasarawa ta yi sabbin shugabanni

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Lemo ta Garin Maraba dake karamar Hukumar Karo a Jihar Nasarawa ta zabi sabbin shugabanninta. An gudanar da zaben ne a ranar…

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Lemo ta Garin Maraba dake karamar Hukumar Karo a Jihar Nasarawa ta zabi sabbin shugabanninta. An gudanar da zaben ne a ranar Litinin da ya gabata a kasuwar, karkashin kulawar shugabannin kungiyar na kasa. Alhaji Babba Ali wanda shi ne ya sanar da sakamakon zaben, ya bayyana cewa wadanda suka samu nasara sun hada da Alhaji Hussaini Abdullahi a matsayin shugaba, da Alhaji Abbas Isah a matsayin mataimakin shugaba, da kuma Abubakar Ahmed Gora  a matsayin Babban Sakatare, yayin da Jibrin Abubakar ya zama Matamakin Sakatare. Sauran su ne Yunusa M. Dahiru  a matsayin Sakataren Kudi da Alhaji Kabiru Ahmed, Mataimakin Sakataren Kudi, da kuma Adamu Gombe wanda ya zama Ma’ajin kungiyar. 

Daga nan sai Alhaji Babba Ali ya bukaci sabbin shugabannin da aka zaba da su tabbatar sun gudanar da harkokin kungiyar bisa gaskiya da rikon amana don tabbatar da dorewar cigaban kungiyar, inda ya kuma jinjinawa ‘ya’yan kungiyar da suka fito kwansu da kwarkwata suka zabi sabbin shugabannin nasu cikin lumana ba tare da tashin hankali a lokacin da kuma bayan zaben ba. 

A nasa bangare da yake jawabin godiya a madadin sabbin shugabannin da aka zaba, sabon shugaban kungiyar, Alhaji Hussaini Abdullahi ya yi godiwa ga magoya bayansa da suka zabe su, inda ya tabbatar musu cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cigaban kasuwar a dukkan matakai. 

Ya kuma yi amfani da damar inda ya bukace su da su ba su cikakken goyon baya don ba su damar kai kungiyar tudun mun tsira. Daga bisani da wakilinmu ya tattauna da sabon shugaban, Alhaji Hussaini Abdullahi ya bayyana cewa tuni ma shi da sauran shugabannin suka tsara wasu mahimman tsare-tsare da a cewarsa za su kawo canji mai ma’ana a kasuwar da zarar sun fara aiki. Wadannan tsare-tsare a cewarsa sun hada da hada kai da sauran bangarorin kasuwar da gwamnatin jihar da na tarayya da kungiyoyi daban-daban wajen bunkasa harkoki da cigaban ‘yan kasuwar baki daya.