Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kano ta yi tir da dukan wani dan jarida da ake zargin dan Majalisar Wakilai Alhassan Ado Doguwa ya yi a jihar.
Sanarwar da shugaban reshen, Abbas Ibrahim da sakatarenrta, Abba Murtala suka sa hannu ta ce, duk da cewa batun na gaban kotu da rundunar ’yan sanda, ya yi fatan a yi binciken kwakwaf kan lamarin.
- Kotu ta rusa zaben Shugaban Masu Rinjaye Ado Doguwa
- An ba hammata iska tsakanin Doguwa da Garo a Kano
“Muna tunatar da ’yan siyasa cewa, ’yan jarida da ’yan siyasa abokan juna ne ta fuskar kawo cigaba na samuwar ingantaccen mulkin dimokurdiyya a shekarar 2023.
“Kyakkyawar dangantar da ke tsakanin Gwmanatin jihar Kano da ’yan siyasa da kuma ’yan jarida a yanzu babu kamarsa, kauce wa hakan ba zai haifar da kyakkyawan sakamako ba,” in ji sanarwar.
Sannan kungiyar ta ce ita ma za ta kafa kwamitin mutum uku don yin wani kwarya-kwaryar bincike na daban domin gano gaskiyar lamarin.
Ana zargin dan majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa da naushin wakilin jaridar Leadership a gidansa yayin wata hira da suka je yi da shi a farkon makon nan.
An ce dan majalisar ya fusata ne a lokacin da suke yi masa tambaya kan zargin da ake yi masa da jifan mataimakin dan takarar gwamnan jihar Kano na Jam’iyyar APC, Murtala Sulen Garo, da kofin shayi, ya ji masa ciwo a hannu yayin wani taro a gidan mataimakin gwamnan jihar Nasiru Yusuf Gawuna.