kungiyar Tsofaffin Ma’aikata da Fansho ta Jihar Kebbi ta yi sababbin shugabanni.
An gudanar da zaben ne a Hotel din Modiyawa da ke Birnin Kebbi a makon jiya.
Sabon Shugaban kungiyar Usman dan Gwari ya bayyana matukar farin cikinsa sakamakon zaben su da aka yi, musamman ma da aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna.
Ya ce: “Da yardar Allah ba za mu ba ku (’yan kungiya) kunya ba, za mu kare hakkokin dukkan ’yan kungiya. Ina fatan za su ci gaba da ba mu goyon baya da hadin kai don samun damar aiwatar da kudurorin da muka sanya a gaba, musamman wajen nemo mana hakkinmu daga wajen gwamnatin jiha da ta tarayya.”
Shugaban kungiyar Fansho na kasa Dokta Abelo O. Afolayan, wanda mataimakinsa na shiyyar Arewa maso Yamma Alhaji Sani Muhammad Sakkwato ya wakilta, ya bukaci Gwamnatin Jihar Kebbi ta hanzarta biyan ’yan fansho kudaden da suke bin ta bashi, ta kuma kara musu kudaden da Gwamnatin Tarayya ta ce za a rika ba su.
Ya nemi Gwamnan Jihar Kebbi Sa’idu Nasamu ya taimaka wa kungiyar da mota bas mai daukar mutum 18 da kuma fili domin gina ofis dinta.
A karshe ya jawo hankalin sababbin shugabannin kungiyar da su kare hakkokin mambobinsu, sannan mambobi su rika ba shugabanninsu hadin kai domin kungiyar ta cim ma nasara.
Sababbin shugabannin sun hada da Alhaji Usman dan Gwari a matsayin Shugaba, sai Ahmad H. dan Kano Mataimakin Shugaba. Shehu Bello Birnin Kebbi shi ne Ma’aji, inda Hassan Muh’d S/Daji shi ne Mai Bincike
Musa Muhammed Gulma da Usman S/Dabai su ne iyayen kungiya.
kungiyar ’yan Fansho ta Jihar Kebbi ta yi sababbin shugabanni
kungiyar Tsofaffin Ma’aikata da Fansho ta Jihar Kebbi ta yi sababbin shugabanni.An gudanar da zaben ne a Hotel din Modiyawa da ke Birnin Kebbi a…