Kungiyar Dalibai, ta tunawa da marigayi tsohon Firayi Ministan Arewa, Alhaji Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Reshen Jami’ar Jos ta karrama fitaccen mai taimaka wa al’ummar nan da ke Jos, Alhaji Abubakar Sadik Plaza, kan ayyukan taimakon jama’a da yake yi a garin Jos da kewaye a ranar Juma’ar da ta gabata.
Da yake jawabi lokacin da yake mika wa Alhaji Abubakar Sadik shaidar karramawar, Shugaban Kungiyar Tunawa da Sardauna, Malam Haruna Yusuf Abba ya ce, ganin irin ayyukan taimakon jama’a da Alhaji Sadik Plaza yake yi, ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba, ya sanya suka karrama shi. Domin ya yi daidai da yadda marigayi Sarduna ya yi, lokacin da yake raye.
Ya ce yanzu babu inda ayyukan taimakon jama’a da Alhaji Sadik Plaza yake gudanarwa bai shiga ba, a cikin garin Jos da kewaye.
Ya ce kadan daga cikin ayyukan taimakon jama’a da ya yi, sun hada da samar da famfunan tuka-tuka a Unguwar Rogo da gina gada a ’Yan Daddawa da gina gada a cikin Kabong.
Har ila yau ya ce akwai asibitoci da dama da ya gyara a cikin garin Jos, kuma yanzu yana nan yana gina wani asibiti, a Garba Daho a garin Jos.
Haka zalika ya ce ya yi famfunan tuka-tuka a wurare da dama a Karamar Hukumar Jos ta Gabas, baya ga daruruwan mutane da yake tallafawa wajen biyan kudaden magani a asibitoci da makarantu.
“Don haka muka karrama shi tare da ba shi sarautar Makama Babba, don karfafa masa gwiwa kan wadannan ayyuka, na taimaka wa al’umma da ya sanya a gaba,” inji shi.
Da yake mayar da jawabi, Alhaji Abubakar Sadik Plaza ya bayyana matukar farin cikinsa, da wannan karramawa da aka yi masa.
Ya ce babban abin da ya karfafa masa gwiwa a ayyukan tallafa wa jama’a, shi ne addinanmu na Musulunci da Kirista sun nuna muhimmancin taimaka wa jama’a.
“A kullum idan na ga wani abu da jama’a suke bukata a shirye nake in taimaka musu, ko a bangaren Musulmi ko a bangaren Kirista. Kuma ina yin wadannan abubuwa ne saboda Allah da kuma fatar ’yan baya su gani su yi koyi,’’ inji shi.
Daga nan ya yi kira ga al’ummar Jihar Filato su ci gaba da zaman lafiya, domin a samu ci gaba a jihar.