A karshen makon da ya gabata ne aka kammala gasar wasan kwallon kafa ta Kofin Murtala Suya a Jihar Kano, inda Kungiyar Sabon Sara Academy ta lallasa takwararta ta Khalid Babies Gwale da ci 2-1.
Gasar, wacce aka fara ta tsawon wata guda an gudanar da ita tsakanin kungiyoyin wasan kwallon kafa 16 da ke cikin birnin Kano kamar yadda Kocin Kamfanin Murtala Suya, Khamis Imam ya shaida wa Aminiya.
Koci Khamis ya kara da cewa “kungiyoyin da suka shiga gasar sun hada da FC Murtala Suya Kabuga da FC Kabuga Young Boys da FC Kansakali da FC Ashafa da FC Dorayi Babba da FC Portugal Rijiyar Zaki da Tudun Yoka Academy da sauransu.
“Mun gudanar da wasan ne ta hanyar fitar da duk kungiyar da aka ci har aka kai matakin karshe, inda aka fitar da kungiyoyi biyu don karawa a tsakaninsu. Kuma mun gudanar da wasan cikin nasara domin babu inda aka sami hatsaniya ko rashin amincewa da sakamako daga bangaren ’yan wasa,” inji shi.
A jawabinsa tun da farko, Alhaji Murtala Muhammad wanda aka fi sani da Murtala Suya ya bayyana cewa ya sanya wannan gasa ce don sanya nishadi tare da debe kewa a tsakanin matasa.
“Mun dauki shekaru uku muna gudanar da wannan gasa wacce muke yi kamar sau uku a shekara da nufin sanya wa matasa nishadi tare da debe musu kewa. Kin san matasa suna son harkar kwallo idan har ka kawo musu harkar kwallo hankalinsu zai tafi wurin, kin ga wannan zai debe wa matasan hankali daga aikata abubuwan da ba su kamata ba kamar su shaye-shaye da sauransu,” inji shi.
Alhaji Murtala ya kara da cewa, “a waje daya kuma muna amfani da wannan hanya domin tallata hajarmu, kasancewar matasa su ne kashin bayan al’umma. Kin san shi mai sana’a yana son sunansa ya kai ko’ina, kasancewar kungiyoyin wasan nan sun fito daga wurare daban-daban a fadin jihar nan, muna sa ran sunanmu zai kai dukkanin wuraren da muke zato.”