✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato

Hare-haren da ake zargin wasu ’yan bindiga ne da suka buɗe wa makiyaya wuta a lokacin da suke kiwo, wanda ke nuna rashin tsaro a…

A wasu rahotanni sun ce an kashe makiyayi guda ɗaya da shanu sama da 100 a wasu hare-haren da aka kai kan makiyaya a wasu ƙauyuka biyu da ke ƙananan hukumomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa a Jihar Filato.

Hare-haren da ake zargin wasu ’yan bindiga ne da suka buɗe wa makiyaya wuta a lokacin da suke kiwo, wanda ke nuna rashin tsaro a yankunan da aka daɗe ana fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, lamarin da ke janyo asarar rayuka.

Sakataren Ƙungiyar Miyetti Allah Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na jihar Ibrahim Yusuf Babayo ya tabbatar da faruwar lamarin tare da zargin ’yan ƙabilar rukunin Berom daga na da hannu wajen kai harin.

Sai dai shugabannin Ƙungiyar matasan Berom sun musanta zargin da ake yi musu, inda suka yi watsi da hakan a matsayin farfaganda.

Daily Trust ta samu rahoton cewa, harin farko ya faru ne da yammacin ranar Talata a unguwar Gero da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu, yayin da na biyu kuma ya faru ne da safiyar Laraba a unguwar Darwat da ke Ƙaramar hukumar Riyom.

A cewar Babayo, makiyaya uku sun samu raunuka a harin na Gero. A halin yanzu ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa na yin jinya a wani Asibiti da ke Jos, yayin da sauran biyun kuma ke jinya a Asibitin Sojoji da ke barikin Rukuba a Jos.

“A ranar 13 ga Mayu, 2025, matasan Berom daga Gero, Gundumar Ngel a Jos ta Kudu, sun haɗa baki suka farwa makiyayan shanu, inda suka kashe shanu kusan 70.

“Sun yanka wasu daga cikin shanun tare da sace naman, sojojin hedikwatar Operation Safe Haɓen sun shiga tsakani suka kama wasu mutane uku da aka samu da naman shanun da aka yanka,” in ji Babayo.

Ya ci gaba da cewa, “A ranar 14 ga Mayu, 2025, matasan Berom a Darwat sun zo da yawa, suka fara harbin shanu na mambobinmu.

“Sun kashe shanu sama da 40, sun yanka wasu, suka kwashe naman, ba tare da wata tsokana ba, haka kawai suka fara harbe-harbe a kan dabbobin, harin da ake zargin an shirya ne, ba mu da wata kariya, na sanar da hukumar rundunar GOC 3 da kuma daraktan tsaro na jihar halin da ake ciki.”

Babayo ya kuma bayyana cewa waɗannan hare-haren wani ɓangare ne na tada hankali.

Ya ƙara da cewa, “A cikin makonni biyun da suka gabata, an samu irin wannan harin inda aka kai wa makiyaya da shanunsu hari, waɗannan hare-haren sun yi sanadin asarar rayukan mutane da kuma satar dabbobi, a ranar Litinin kaɗai, an ce an samu ɓacewar wani makiyayi, an kuma yi awon gaba da shanu 41 a Bisichi.”

“A kullum ana kashe mu, da alama ana tsokanar mu, muna kira ga gwamnati da ƙasashen duniya da su lura da abin da ke faruwa a Jihar Filato, a matsayinmu na ’yan ƙasa masu bin doka, muna kira ga mambobinmu da su kwantar da hankalinsu, muna kuma kira ga hukumomin tsaro da su kawo ƙarshen wannan kashe-kashe na rashin hankali da kuma kare Fulani makiyaya daga ci gaba da kai hari,” in ji Babayo.