A karshen makon da ya gabata ne kungiyar Ma’aikatan Gidan Rediyo da Talabijin da Harkokin Nuna Al’adu (RATTAWU), reshen Hukumar Adana Kayan Tarihi ta Jihar Kano, Gidan dan Hausa (History and Culture Bureau) ta gudanar da zabe tare da rantsar da sabbin shugabanninta.
A jawabinsa tunda farko, Shugaban kungiyar RATTAWU na Jihar Kano, Malam Mohammed Musa Nya ya yi kira ga sabbin shugabannin da su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da Allah Ya dora musu na shugabancin kungiyar.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Hukumar Adana Kayan Tarihi ta Jihar Kano, Dokta Maisara Nuhu Wali kira ya yi ga ma’aikatan hukumarsa, wadanda suka hada da zababbun shugabannin wannan kungiya da su hada kai da juna wajen ciyar da gidan tarihin na dan Hausa gaba, duba da irin kulawa da gwamnatin Jihar Kano ke ba ma’aikatan gidan.
Shugabannin da aka zaba sun hada da Kabiru Musa Bichi, a matsayin shugaba; da Nasiru Abdullahi Maikano, a matsayin sakatare; da Nasiru Garba, a matsayin Mataimakin Sakatare; da Nafi’u Nasidi Mohammad, a matsayin ma’aji; da Abdurrahman Mohammad, a matsayin Sakataren Kudi; da Yahaya Maitama, a matsayin Mai Binciken Kudi; da kuma Zangina A. Jibril, a matsayin jami’in hulda da jama’a.
Har ila yau a wajen wannan taro an rarraba takardun yabo ga shugabannin kungiyar masu barin gado tare da gode musu bisa jagorancin kungiyar na tsawon shekaru biyu da suka yi.
kungiyar RATTAWU, HCB ta zabi shugabbanninta
A karshen makon da ya gabata ne kungiyar Ma’aikatan Gidan Rediyo da Talabijin da Harkokin Nuna Al’adu (RATTAWU), reshen Hukumar Adana Kayan Tarihi ta Jihar…