kungiyar malaman makarantun sakandare da firamare ta kasa (NUT) reshen Jihar Yobe ta nuna rashin jin dadin ta dangane da kara lokacin bude makarantun kasar nan da ma’ikatar ilmi ta tarayya ta yi, saboda tsoron yaduwar cutar Ebola.
Shugaban kungiyar Kwamared Muhammad Lawan Ibrahim a tattaunawarsa da Aminiya dangane da kara lokacin hutu zuwa ranar 13 ga watan Oktoba 2014 da Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau saboda tsoron yaduwar cutar Ebola.
Ya ce tun da yake umarnin kara wa’adin hutun da gwamnatin tarayya ta bayar ya shafi dukkan kasa ne, to za su kasance masu biyayya da shi.
Ya ce a ganinsu gwamnatin tarayya ta yi hakan ne kawai don a ci gaba da nisanta ’ya’yan talakawa samun ilimi mai inganci musamman wadanda ke arewacin kasar nan.
“Duk da tsawon lokacin da Jihar Yobe da ma sauran jahohin da ke makwabtaka da ita suka shafe wajen fama da matsalar tabarbarewar harkar tsaro, amma gwamnatin tarayya ba ta taba tunanin ba da irin wannna umarni ba sai da cutar Ebola ta barke. Har yanzu ba a ba mu wannan umarnin a rubuce ba, muna ji ne kawai a kafafan yada labarai.” Inji shi.
kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan dukkan matsalolin da ke addabar kasar nan, musamman tabarbarewar harkar tsaro da ke addabar sassan arewacin kasar, ba kawai a ba da muhimmanci ga cutar Ebola ba.
A karshe ya shawarci iyayen yara su dauki karin lokacin hutu da gwamnatin tarayyar ta yi a matsayin kaddara, musamman a Arewa maso Gabas yankin da ke baya dangane da tabarbarewar harkokin ilmi, saboda halin da yankin ya shiga kan matsalar tsaro.
kungiyar NUT ta yi korafi kan kara wa’adin hutun makarantu
kungiyar malaman makarantun sakandare da firamare ta kasa (NUT) reshen Jihar Yobe ta nuna rashin jin dadin ta dangane da kara lokacin bude makarantun kasar…