✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila

A dimokuraɗiyya ana buƙatar hamayya mai ƙarfi, domin idan babu hamayya mai ƙarfi, za mu iya faɗawa siyasar jam’iyyar ɗaya.”

Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ’yan hamayya a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Nijeriya.

Ya bayyana cewar haɗaka ’yan adawar za ta taimaka wajen hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a Jihar Legas a jiya Asabar a mazaɓarsa da ke Surulere.

Sai dai tsohon shugaban Majalisar Wakilan ya bayyana shakkunsa kan haɗakar, inda ya ce ce ba ya tunanin za ta yi wani tasirin a-zo-a-gani.

“Muna maraba da samar da haɗakar. Ai ba wannan ba ne karo na farko da aka samu haɗakar ’yan siyasar a wannan ƙasar tamu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “a dimokuraɗiyya ana buƙatar hamayya mai ƙarfi, domin idan babu hamayya mai ƙarfi, za mu iya faɗawa siyasar jam’iyyar ɗaya,” in ji shi.

A bayan nan ne dai wasu fitatun ’yan jam’iyyun hamayya ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi da sauransu suka ayyana jam’iyyar haɗaka ta ADC domin fuskantar Zaɓen 2027, inda suke fatan za su kayar da Bola Tinubu.