Daraktan Kungiyar musulmi (MURIC) Farfesa Ishaq Akintola, ya bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta yi duk mai yuwa wajen samar da wadataccen man fetur lokacin bikin kirsimeti.
Akintola, ya yi kiran ne yau a jihar Legas, ya shawarci masu dakon man fetur da Gwamnatin Tarayya akan bin matakan da zai dakile kawo karancin man fetur lokacin kirsimeti a yankunan Najeriya.