✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Miyetti Allah za ta magance fadace-fadacen tsakanin Fulani da Tibi -Ardon Zuru

kungiyar Miyetti Allah, a karkashin jagorancin Albino Muhammadu Kirowa (Ardon Zuru) ta kuduri aniyar gano bakin zaren matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa…

kungiyar Miyetti Allah, a karkashin jagorancin Albino Muhammadu Kirowa (Ardon Zuru) ta kuduri aniyar gano bakin zaren matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Alhaji Muhammadu Ardon Zuru, wanda shi ne sabon zababben shugaban Hadaddiyar kungiyar Miyetti Allah na kasa, ya yi wannan bayanin ne a garin Birnin Kebbi a zantawarsa ta farko da manema labarai bayan samun nasarar zabensa da aka yi a matsayin sabon shugaban kungiyar a karshen makon da ya gabata.
Ardon na Zuru ya ce wadansu ne ke cin ganimar fada tsakanin Fulani da manoma, musamman babbar matsalar da fi damun Fulani ita ce wadda ta shafi fada da ’yan kabilar Tibi, lamarin da yanzu kungiyar Miyetti Allah ta lashi takobin gano tare da warware bakin zaren.
Ya ce  babu wani dalilin yin fada tsakanin Fulani da ’yan kabilar Tibi, musamman saboda a tarihin ’yan uwantaka, ba dangantakar da ta kai ta tsakanin Fulani da Tibi, kuma kodayake a baya an sami matsalar shugabanci, inda wadansu suka shigo suka mayar da hada fada tsakanin  al’umma wata hanyar samun kudi, “Wannan ya kau daga yanzu. Fulani da Tibi ’yan uwa ne illa dai akwai wadansu mutane da ke cin moriyar wannan rashin zaman lafiya, wanda, cikin yardar Allah, za mu yi maganinsa”. Inji shi.    
Ya kuma sha alwashin magance matsalar da Fulani ke fama da ita ta cinye musu matsugunai da burtaloli a kasar nan, wanda yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya Fulani suke barin kasar nan zuwa wadansu kasashen Afirka.
 Ardon ya kuma yaba wa mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Sa’adu Abubakar wajen ganin an tabbatar da adalci a cikin gudanar da zaden wadanda za su jagoranci kungiyar, saboda haka ya yi kira ga ’yan Nijeriya, musamman ’ya’yan kungiyar a ko’ina suke da su bayar da gudummawarsu wajen ciyar da ita da kuma kasa baki daya gaba, ta kowane bangare za su iya.
A karshe ya bukaci a ba shi kyawawan shawarwarin da za su taimaka wajen bunkasar kungiyar kuma in za a yi kowane irin korafi, akwai bukatar a yi mai ma’ana.