✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar mata maharba ta yi sabuwar shugaba a Arewa maso Gabas

An yi nadin nata ne a fadar Sarkin Zing, da ke jihar Taraba

Shugaban Kungiyar Maharba na Kasa, Alhaji Muhammed Umar Tola, ya nada Habiba Isa a matsayin Shugabar matan kungiyar ta yankin Arewa maso Gabas.

An nada Malama Habiba Isa ne a fadar Sarkin Zing da ke Jihar Taraba ranar Asabar.

Shugaban kungiyar maharba na kasa ya shawarci sabuwar Shugaban matan kungiyar da ta rike aikin da kyau tare da mayar da hankali wajen taimaka wa jami’an tsaro a aikinsu na yaki da masu aikata laifuka, musamman fashi da satar mutane.

Da take jawabi bayan nadin nata, Malama Habiba Isa, ta dauki alkawarin bayar da gudunmawarta wajen taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da aikata laifuka a yankin.

Dubban maharba daga sassa daban-daban na jihohin yankin Arewa maso Gabas din ne suka halarci bikin nadin.