kungiyar mahauta ta karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi ta gudanar da bikin kaddamar da sababbin shugabanninta a garin Magama Gumau kwanan baya.
Da yake jawabi a wajen bikin, dan majalisar dokoki ta Jihar Bauchi, mai wakiltar mazabar Toro da Jama’a, Alhaji Tukur Ibrahim ya bayyana cewa kungiyar mahauta tana da matukar mahimmanci a tsakanin jama’a, lamarin da ya sa yake tare da ita.
Ya ce idan babu biyayya shugabanci ba zai tafiyu ba, don haka ya yi kira ga ’yan kungiyar su cigaba da yi wa wadannan shugabanni da aka zaba biyayya.
Daga nan ya ba da tabbacin cewa zai yi kira ga gwamnati kan ta tallafa wa wannan kungiya.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar mahauta ta Jihar Bauchi, Alhaji Baba Sarkin Fawa ya yi kira ga sababbin shugabannin kan su ji tsoran Allah su yi adalci ga ’yan wannan kungiya da al’umma gabaki daya.
Har ila yau ya yi kira a gare su kan su wayar wa mahauta kai kan a tabbatar da ana samun dabbobi masu kyau da lafiya don yankawa. Ya ce, “Ku tsaya wajen ganin dukkan dabbar da ba a yarda da ita ba, kada a yanka ta a sayar wa jama’a naman”.
Daga nan ya yi kira ga mahautan karamar hukumar ta Toro kan su cigaba baiwa wadannan shugabanni goyon baya da hadin kai don a cimma nasara, sannan ya bukaci su mayar da hankali wajen sanya ’ya’yansu a makaranta, kuma su ma kansu iyaye su rika neman ilimi domin sana’a ba ta hana karatu, “Don haka ku yi kokari ku rika sanya ’ya’yanku a makaranta”. Inji shi.
A nasa jawabin sabon shugaban kungiyar, Alhaji Amadu Saleh Tulu ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan goyon baya da mahautan suka ba shi, saboda haka ya ba da tabbacin shi da sauran wadanda aka zaba za su yi iyakar kokarinsu wajen rike wannan amana da aka damka masu.
Ya ce, “Za mu kawo cigaba a kan harkokin wannan kungiya a wannan karamar hukuma”.
kungiyar mahauta ta karamar Hukumar Toro ta samu sababbin shugabanni
kungiyar mahauta ta karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi ta gudanar da bikin kaddamar da sababbin shugabanninta a garin Magama Gumau kwanan baya.Da yake…