Ma’aikatan Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, sun zabi sababbin shugabannin Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Najeriya (NULGE) reshen karamar hukumar.
Ma’aikatan sun gudanar da zaben sababbin shugabanninsu ne a Sakatariyar Karamar Hukumar da ke garin Saminaka a karshen mako.
Sababbin shugabannin da aka zaba, sun hada da Jamilu Sani a matsayin Shugaba da Bako Kawu, Mataimakin Shugaba da Ahmed Abdullahi Sakatare da Stephen Garba Mataimakin Sakatare da Abdul Munka’ila Ma’aji da Akilu Yarima Dattijon Kungiya da Serah Ishaya Shugabar Mata.
Sauran su ne Nura Abdullahi, Mai Binciken Kudi da Hamisu Ibrahim Wakilin Sashin Harkokin Mulki da Kudi da Usman Yet, Wakilin Sashin Ayyuka da Sama’ila Ahmed Wakilin Sashin Noma da Salmanu Umar, Wakilin Sashin Ilimi da Walwala da kuma Ibrahim Jamilu Abubakar, Shugaban Matasa na Ma’aikatan.
Da yake jawabi a wajen Daraktan Ma’aikata na Karamar Hukumar Lere, Alhaji Adamu Gubuci, ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda aka gudanar da zaben lafiya.
Ya yi kira ga sababbin shugabannin da aka zaba su yi adalci, kan wannan zabe da aka yi musu. Ya yi addu’a ga shugabannin kan Allah Ya taimake su bisa wannan aiki da aka dora musu, kuma Ya sanya su gama lafiya.
A jawabin, Shugaban Kungiyar NULGE, reshen Jihar Kaduna, Kwamared Rayyanu Isiyaku Turunku, ya ce babu shakka ma’aikatan Karamar Hukumar Lere sun zabi shugabannin da suke so, don haka ya yi fata shugabannin za su tallafa wa ma’aikatan karamar hukumar.
Shugaban wanda Shugaban Kungiyar na Karamar Hukumar Birnin Gwari, Kwamared Shu’aibu Jibrin, ya wakilta, ya yi kira ga ma’aikata su rika zuwa aiki a kan lokaci kuma su rika zama a wurin aiki, har zuwa lokacin tashi.
Sa’annan ya kirayi ma’aikatan kananan hukumomin Jihar Kaduna su ci gaba da kasancewa masu biyayya kamar yadda aka sansu.
A jawabinsa a madadin wadanda aka zaba, sabon shugaban kungiyar, Jamilu Sani, ya mika godiyarsu ga Allah, da kuma dukkan ma’aikatan karamar hukumar kan wannan zabe da aka yi musu. Ya ce babu shakka wannan wata rana ce mai matukar tarihi a gare su, saboda jama’a sun fito sun zabi shugabannin da suke bukata.
Ya ce saboda kyakyawan zaton da ake yi musu ya sa aka zabe su, don haka da yardar Allah za su ba marada kunya, wajen ganin sun gudanar da ayyukansu tsakani da Allah.
Ya yi kira ga ma’aikatan su ci gaba da ba su goyon baya da hadin kai kuma su ci gaba da yi musu addu’a.