Kwamared Muhammad Aminu Umar shi ne sabon shugaban kungiyar kwadago reshen Jihar Sakkwato a tattaunawarsa Aminiya ya yi karin haske game da mayar wa da mata martabarsu da yadda ya samu nasarar dare wa shugabanci kungiyar da sauran batutuwa: Ga yadda zantawar ta kasance:
Aminiya: Kai ne sabon shugaban kungiyar kwadago reshen Jihar Sakkwato wadan ne abubuwa ne kake ganin sun taimaka wajen samun nasararka.
Kwamared Muhammad Aminu: Bismillahi da farko dai sunana Kwamared Muhammad Aminu Umar shugaban kungiyar Majinyata da Unguwar Zoma ta Jihar Sakkwato yanzu kuma sabon shugaban kungiyar kwadago ta jihar, Alhamdulillah na san akwai abubuwa da dama da suka bai wa mutane sha’awa lokacin mulkin da muka yi a baya na kungiyarmu. Ba ni kadai ba duk nasarorin da muka samu idan ba goyon bayan mutanenmu, nasarar ba za ta samu ba, kamar fadi tashin da muka yi kan gyaran albashin ma’aikatan jinya na kowane mataki daga jiha zuwa kananan hukumomi Allah Ya taimakemu muka samu fahimtar juna tsakaninmu da gwamnati aka yi nasara. Saboda mun gina abin bisa gaskiya, ba wani son rai ganin yadda jihar tamu take ciki muka yi wa kanmu adalci aka biya bukatun ma’aikatan, da yawa kuma ban daukar ra’ayina akan zartar da hukunci ne bisa ga yardar kowa domin bani da wani ra’ayi wanda ya fisu.
Ni kawai jagora ne, dole kuwa shugaba ya kiyaye hakkin al’ummar da yake jagoranta, domin kada wani abu ya taso za a yi masu bayani saboda aikata abin da ya dace ba wanda suke so ba. Muna fatan Allah Ya taimakemu mu ci gaba da yin hakan domin daurewar nasara ta wannan aikin da aka daura mana.
Aminiya: Ma’aikatan jihar nan suna cikin bukatar samun walwala da karin girma, ko kana da wani shiri na ganin bukatarsu ta biya.
Kwamared Muhammad Aminu: Kamar yadda na yi ma bayani ita kungiya za ta yi aiki bisa ga yadda doka ta tanada haka ake tunanin gwamnati ta yi, kan hakan ka ga dole ne kungiya da gwamnati su tanadi wata matsaya da muka haduwa don warware matsalolin ma’aikata da samo fahimtar juna ga wadanda ba su yiwuwa, kamar yadda ka yi magana nasan Jihar Sakkwato na cikin jihohin da ke kokarin inganta ma’aikatansu da ba su hakokinsu iya gwargwado, wannan gwamnati mai barin gado ta yi kokarin sosai ga ma’aikatanta wajen ba su kwarin gwiwa. An raba masu babur da motoci da gidaje, kasan idan dambu ya yi yawa baya jin mai dole akwai wasu wurare da ake bukatar gwamnati ta kula da su domin korafe-korafe sun yi yawa.
Bayan na dare bisa wannan kujera na fara nazarin abubuwan ne kafin a kawomin kukan, a wurin bukinmu na ranar ma’aikata mun ba kowace kungiya ta gabatar da korafinta don mu fuskanci hukuma. Wasu ababen ma ba su bukatar kudi kulawa kawai suke bukata.
Kan batun karin girma ga ma’aikata bai kamata ya zama matsala ba domin abu ne da aka sani duk bayan shekara uku ya kamata ma’aikaci ya bar matakin da yake zuwa wani mataki na gaba, idan akwai wani dalili rashin kulawar ma’aikaci ga aikinsa ko wani abu daban to, ko daga ita hukuma ce za ta mayar ma da karin kudinka ma’ana ariyas to hakan baya faruwa wannan kalubale ne ga ma’aikata mutum ya fi shekara uku yana jiran karin girma, amma shiru kuma idan an yi masa ba wani kari da za a yi masa wahalarsa ta tafi a banza ka ga an tauye masa hakki tun da karin girma ba ma’aikaci ke yi ma kansa ba ma’aikata ce ko gwamnati, duk dalilin da ya sanya suka rike karin girmansa to yakamata a kula baya don hakkin mutum ne.