kungiyar kwadago ta Najeriya reshen Jihar Neja ta bullo da sabon tsarin da zai saukaka wa ma’aikatan gwamnatin jihar mallakar sababbin motoci.
Shugaban kungiyar Kwamred Idris Yahaya Ndako wanda Kwamred Sani Yunusa Adamu ya wakilta ne ya sanar wa Wakilan rassan kungiyar a Minna a makon jiya.
Ya ce kungiyar ta kulla yarjejeniya da kamfanoni harhada motoci na PAN da ke Kaduna da kuma na KIA don samar wa ma’aikatan sababbin motoci.
Ya ce kudin motocin ya kama daga Naira miliyan 1 da dubu 900 zuwa kasa, inda za a ba ma’aikatan damar biya a hankali cikin shekara 4.
Shugaban kungiyar kwadago ta Trade Union Congress reshen Jihar Neja Kwamred Kabiru Tanimu ya jaddada kudurinsu na nazarin yarjejeniyar da za ta taimaka wa ’ya’yanta.
Ya ce kofa a bude take ga kowane dan kungiya da yake so ya ba su shawarwarin da za su taimaka musu ta kowace fuska, inda ya ce nan da lokaci kadan za a baje-kolin motocin a sakatariyar Gwamnatin jihar.
Wasu daga cikin ma’aikatan da wakilin Aminiya ya yi hira da su sun yaba wa wannan tsarin.
kungiyar kwadago ta fitar da tsarin da ma’aikata za su mallaki motoci a Jihar Neja
kungiyar kwadago ta Najeriya reshen Jihar Neja ta bullo da sabon tsarin da zai saukaka wa ma’aikatan gwamnatin jihar mallakar sababbin motoci.Shugaban kungiyar Kwamred Idris…