kungiyar Katsina Mazuna Jihar Legas ta umurci ’yan asalin jihar ta Katsina mazauna Legas da kowa ya samu katin shaidar cewa shi dan jihar Katsina ne domin guje wa wulakanci daga jami’an tsaro ko jami’an jiha ko kuma na gwamnatin tarayya.
Shugaban kungiyar na Jihar Legas, Alhaji Abubakar Sanusi Faskari ya ce sun ba da wannan umurnin ne biyo bayan halin tsaro da kasar ke fama da shi kuma hakan yana taimakawa, domin da katin ne mutanensu suka tsallake kame ko wulakanci iri daban-daban a duk fadin jihar har ma da jihohi makwabta.
Ya ce da farko wasu daga cikinsu ba su dauki wannan shawarar da muhimmanci ba, sai da wadanda suka yi suke fada musu amfaninta. “Mun samar da wannan tsarin ne domin ta haka kadai za a samu saukin tantance mutanen jihar da kuma wace irin sana’a mutun ke yi kuma daga wace karamar hukuma yake a jihar ta Katsina.
Shugaban ya ce sun tsara abin ne unguwa-unguwa kana sai an tantance ka an samu wadanda suka sanka kuma suke da tabbacin kai dan jihar Katsina ne kana a ba ka katin shaidar, wanda ake biyan yadda mutanen kowace unguwa suka tsara a kansa.
Ya ce bayanan da ke kunshe a katin, wanda ke da tsari iri guda, sun kunshi suna; karamar hukumar da ka fito; unguwar da kake a Legas, sai kuma sa hannun shugaba.
Taron, wanda suka yi shi a gidan mallakar gwamnatin Jihar Katsina da ke kan titin Kofo Abayomi da ke unguwar bictoria Island, ya samu halarcin wakilai daga daukacin unguwannin da ke fadin jihar.