✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar kare hakkin masu rike da sarauta ta nemi a guje wa cin zarafin shugabanni

kungiyar kare hakkin masu rike da sarautun gargajiya, reshen Jihar Bauchi, ta shawarci jama’a su guje wa cin zarafin shugabanni don su kasance masu albarka…

kungiyar kare hakkin masu rike da sarautun gargajiya, reshen Jihar Bauchi, ta shawarci jama’a su guje wa cin zarafin shugabanni don su kasance masu albarka da cika alkawari wajen sauke nauyin da ya dora  a kansu.
Shugaban kungiyar, reshen Jihar Bauchi, Alhaji Awwal Galadima, dansaran Bauchi shi ne ya bayyana haka cikin wani taron manema labarai da ya kira a Bauchi. Ya ja hankalin jama’a su nisanci yin hassada da cin zarafin masu rike da mukaman siyasa da kuma sarakunan gargajiya. Jama’a su kasance suna yi musu addu’o’in fatan alheri ko da sun yi kuskure ne, domin yin hakan shi ne zai sa su kasance kan tafarkin da ya dace, tare da nuna adalci da tausayi a yayin da suke gudanar da jagorancin da suke kai.
dansaran Bauchin ya bayyana haka ne don jan hankalin mutanen da ke shiga kafafen watsa labarai suna cin zarafin shugabanni, kamar yadda ya bayyana cewa bai ji dadi ba yadda aka shiga cikin wasu kafafen labarai da jaridu ana cin zarafin tsohon akawun majalisar dokokin Jihar Bauchi, Alhaji Ya’u Mohammed Gital, wanda a halin yanzu shi ne shugaban ma’aikata na Ministan Abuja, Alhaji Bala Mohammed, kauran Bauchi.
Ya kara da cewa matukar mutanen Jihar Bauchi da ma Arewa gaba daya, za su ci gaba da kasancewa masu cin zarafin shugabanni, to ba za a ci gaba yadda ake so ba. Saboda bai dace ba a rika dauko gidan shugaba da wasu sirrin iyalansa ana bugawa don cin zarafi da nuna hassada a fili, alhali wasu daga cikin irin wadannan zargi ba gaskiya ba ne. Yin haka na iya haifar da gaba tsakanin shugabanni da talakawa, haka kuma taimakon da wasu marasa karfi ke samu daga irin wadannan shugabanni zai iya kasancewa sun daina samu, sun guje wa mutanensu don ganin komai suka yi ba sa tsira daga cin zarafin jama’ar da suke jagoranta.
Alhaji Awwal Galadima ya shawarci jama’a, a duk inda suke, idan sun ga shugabanninsu kan kuskure su rika rubuta takarda suna tura musu don ba su shawara, kuma su rika bin su da addu’a don su samu kamanta adalci da gyara kurakuransu. Haka su ma shugabannin idan an ba su shawara su rika dauka su gyara kuskuransu, kar su lura da cewa an yi haka ne don neman wani abu a wajensu, hakan shi ne zai albarkaci matsayin da suke kai su kuma samu ci gaba mai albarka sakamakon addu’ar fatar alheri da talakawa ke bin su da ita.