✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Izala ta yi taron kara wa juna sani a Jos

kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta  kasa (JIBWIS) ta shirya wa shugabanni shirya gasar karatun Alkura’ani Mai Girma na reshen jihohin kasar nan, taron…

kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta  kasa (JIBWIS) ta shirya wa shugabanni shirya gasar karatun Alkura’ani Mai Girma na reshen jihohin kasar nan, taron karawa juna sani, a garin Jos babban birnin Jihar Filato.
Da yake jawabi a wajen rufe taron Shugaban Majalisar Malamai ta kasa na kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga al’umma kan a rika yin aiki da ilimin da aka koya.
Ya ce “duk ilimin da aka koya idan ba a aiki da shi ya zama marar amfani. Don haka ya yi kira ga mahalarta taro kan su je su yi aiki da abubuwan da aka koya masu a wajen taron.”
Har’ila yau, ya yi kira ga al’ummar Musulmi kan su rika  gina da’a  da zumunci a tsakanin al’umma ta hanyar kaiwa ‘yan uwa ziyarar sada zumunci. Ya ce Al’kur’ani Mai Girma ya nuna cewa raya zumunci wajibi ne. “Don haka mu je mu koya wa ‘ya’yanmu da matanmu sada  zumunci.”
Tun da farko a nasa jawabin Babban Jami’in Gudanar na Gasar Ustaz Aminu Yusuf Nuhu ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne domin su ilimantar da shugabannin gasar
karatun Alkura’ani mai girma na jihohi yadda za a  shirya gasar karatun Alkur’ani a wannan shekara a matakan rassa da kananan hukumomi da kuma jihohi. Ya ce sun shirya  taron ne don ilimantar da shugabannin  yanayin yadda aikice-aikace kungiyar  yake a ofisoshinsu.
“Babban burinmu kan kirkiro wannan shiri shi ne  mu kara zaburar da shugabanni wannan kungiya kan ayyukan ofisoshinsu don a samu nasara,” inji shi.