Dubban mutane ne daga sassan Najeriya suka yi wa garin Hadeja na Jihar Jigawa tsinke domin bikin aza harsashin ginin jami’ar Musulunci ta farko a garin mai suna Assalam Global University.
Gina jami’ar yunkuri ne na Kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis-Sunnah (JIBWIS), wacce aka fi sani da Izala a Najeriya na ganin ta kafa jami’a mallakin kanta.
- Buhari ya jinjinawa Izala kan habaka ilimi
- Izala ta kaddamar da gidauniyar neman ayyukan shekara a Abuja
Yayin bikin, an sami tallafin sama da Naira biliyan daya daga gwamnoni, ’yan majalisu, ’yan kasuwa da sauran jama’a.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa, ya bayar da tallafin miliyan N250 a madadin takwarorinsa na jihohin Kano, Sakkwato, Kebbi, da kuma Katsina yayin da wani da bai amince a ambaci sunansa ba ya bayar da miliyan N500.
’Yan Majalisar Dokoki ta Kasa sun bayar da miliyan N150, yayin da uban jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya bayar da miliyan 10.
Da yake jawabi tun da farko, Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce makasudin gina jami’ar shi ne a ba matasa damar samun ilimin zamani domin a su sami ingantacciyar rayuwa.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa jami’ar ba ta Musulmai kadai ba ce, kowa na iya neman gurbin karatu a cikinta matukar ya cika sharuddan samun gurbin karatu.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Isa Ali Pantami ne ya wakilci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a taron inda ya jaddada kudurin Gwamnatin Tarayya na ba harkar ilimin fifiko.
Shi kuwa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar wanda shi ne ya jagoranci aza harsashin ginin ya ja hankalin masu rike da mukaman siyasa kan bukatar cika alkawuran da suka dauka, yana mai cewa kowannensu zai amsa tambaya kan yadda ya gudanar da mulkinsa a ranar lahira.