Kungiyar Dangin Juna Afirka Initiatibes (DJAI) da aka kafa shekara biyar da suka wuce don taimakon marayu da marasa galihu a taronta karo na biyar a garin Bauchi, ta koya wa malaman tsangaya muhimmancin bada agajin farko wato da koya musu yadda za su kare almajiransu daga kananan cututtuka, inda ta ba su akwatunan magani na taimakon farko tare da rabaw a almajirai400 tabarmi da barguna da takalma da kwanukan robobi da sabulan wanka da wanki da yadi biyar-biyar.
A jawabin bako na musamman, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Alhaji Abubakar Sadik Ibrahim Kurba, ya jinjina wa kungiyar kan wannan kokari nata da ya ce abin koyi ne.
Ya ce jihohin Bauchi da Gombe jihohi ne da suke da niyyar taimaka wa marasa galihu wanda hakan ne ya sa dukkansu suka kirkiro da shirye-shirye da dama don share wa masu karamin karfi hawaye.
Ya yi kira ga daidaikun jama’a da masu hannu da shuni da akalla kowane mutum ya dauki almajiri daya domin taimaka masa, inda ya ce hakan zai sa a samu fadadar irin wannan tallafi.
Sai ya yi kira ga mutane su daina cin zarafin almajirai domin su ma ’ya’ya ne da bai kamata a ci mutuncinsu ba, inda ya kawo misali da wanda ya kona almajiri a magasar burodi a garin Bajoga a Jihar Gombe.
Babban Bako a wajen taron, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Alhaji Abubakar Y. Suleiman, Dan Galadiman Ningi, yaba wa kungiyar ya yi inda ya ce ta yi abin a yaba.
Ya yi kira ga jama’a su yi koyi da abin da kungiyar ta yi na share wa almajirai hawaye, domin ba su kwarin gwiwar yin karatunsu na Alkur’ani Mai girma cikin natsuwa.
Kan batun da Shugaban Alarammomin Ysangaya ya yi cewa gwamnatin Bauchi da ta gabata tana ba su alawus din Naira dubu 10 amma yanzu ya tsaya, ya ce zai gaya wa Gwamna kuma ya tabbata zai duba, domin a ci gaba da ba su.
A jawabin Shugaban Kungiyar DJAI, Bashir Sani Dogo, ya ce sun kafa kungiyar ce don tallafa wa marasa galihu, inda duk shekara suke taruwa a tsakaninsu su hada gudunmawa su sayi kaya su raba.
Ya ce kafin wannan taron sun yi irinsa a jihohin Kaduna da Neja da Kano da kuma Bauchi nan gaba kuma za su zauna su ga jihar da ta dace su kai wannan tallafi duk da Shugaban Majalisar Jihar Gombe ya nemi idan shekara ta juyo su yi taron a Gombe.