✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kungiyar Bayern Munich ta dawo wasanni da kafar dama

Kungiyar kwallon Kafa ta Bayern Munich da ke kasar Jamus ta dawo wasan Bundesliga da kafar dama inda takai ziyara kuma ta samu nasara akan…

Kungiyar kwallon Kafa ta Bayern Munich da ke kasar Jamus ta dawo wasan Bundesliga da kafar dama inda takai ziyara kuma ta samu nasara akan kungiyar Union Berlin da ci 2-0 a ranar Lahadi.

Dan wasan gaba na kungiyar Robert Lewandowski ne ya fara jefa wa kungiyar ta Munich kwallo a minti 40 da fara wasan a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Ana saura minti 9 da kammala wasan ne mai tsaron baya na kungiyar Benjamin Pavard ya kara kwallo ta biyu wanda ya tabbatar wa kungiyar nasara a wasanta na farko bayan da aka dawo daga hutun coronavirus a kasar ta Jamus.

Kungiyar Bayern Munich zata ci gaba da kasancewa a kan teburin gasar da maki 58 a saman Burossia Dortmund mai maki 54.

A wasan da aka buga tun farko a yau dai an tashi canjaras tsakanin kungiyoyin Cologne da Mainz da ci 2-2.