Babban Daraktan Cibiyar Samar da Zaman Lafiya da Magance Rikici (ICPR), Dokta Bakut Tswah Bakut ya yi kira ga sarakunan gargajiya da sauran jama’a su zamo jakadun zaman lafiya a cikin al’umma.
Dokta Bakut ya yi wannan kira ne yayin wata ziyara da ya kai ga sarakunan gargajiyar da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.
Dokta Bakut ya jajanta kan rashin tsaro da ya addabi sassan Najeriya, inda ya bukaci sarakunan su hada kai da gwamnati domin shawo kan matsalolin tsaro da ya ce wannan gwamnati ta sanya a gaba.
Daraktan ya bayyana ziyarar tasa da ganawa da masu ruwa-da- tsaki wajen gina zaman lafiya a kananan hukumomin Jaba da Zangon Kataf a matsayin wani yunkuri na Gwamnatin Tarayya don cimma burinta na wanzar da zaman lafiya.
A jawabinsu a lokuta daban-daban, Agwam Bajju, Malam Nuhu Bature da Sarkin Kamantan, Mista Adamu Alkali da Sarkin Ikulu, Mista Yohanna Sidi Kukah da Agwam Atyap, Mista Dominic Gambo Yahaya, sun yaba wa matakin na gwamnati, inda suka ce tuni suke jiran irin wannan lokaci daga gare ta, tare da alwashin mara wa shirin baya don wanzar da zaman lafiya a yankunansu.
A karshe sarakunan sun jinjina wa dan majalisarsu da ke wakiltar kananan hukumomin Jaba da Zangon Kataf, Mista Amos Gwamna Magaji wanda ya shirya wannan ganawa.