✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da Aminu Bayero ba zai iya jagorantar hawan Sallah ba — Kurawa

Ba zai yiwu ka yi hawa ba idan ba ka zaune a Gidan Rumfa wanda a tarihi da kuma al’ada daga nan ake fitowa.

Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne.

A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira gudun tayar da hargitsi a Jihar Kano.

Gabanin yanzu dai, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da shi kansa Sarki Aminu sun ɗaura azama ta gudanar da haye-hayen sallah bana.

Sai dai da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Kurawa ya bayyana cewa tun farko Sarki Aminu ba zai iya gudanar da hawan Sallah ba, saboda an riga da tuɓe masa duk wata cancanta da wasu ka’idoji da matakai da ke da alaƙa da wannan al’adar ta hawa da ake bai wa Sarki don girmamawa.

Ya bayyana sanar da janye hawan da Sarki Aminu ya yi a matsayin wani lamari na siyasa da kuma wani yunƙuri na janyo abin magana a jihar.

Kurawa, wanda shi ne marubucin littafin nan ɗaya tilo kan tarihin hawan Sallah a Kano, da har Hukumar Kula da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ke ba da misali da shi kan hawan Sallar Kano a matsayin al’adu na duniya, ya jaddada cewa bikin hawan Sallah wata al’ada ce da ake gudanarwa bisa tsari tun sama da shekaru 500 da suka gabata.

Ado Kurawa ya bayyana cewa a bisa tsari na al’adar Durbar, duk wani hawan Sallah ba ya cika sai da goyon bayan ’yan majalisar masarauta irin su Shamaki, Ɗan Rimi, Madakin Shamaki, Madakin Dan Rimi, da Sallama.

Saboda haka a cewar Kurawa, Sarki Aminu ba shi da waɗannan ’yan majalisa da za su tabbatar da cikar hawan sallah kamar yadda al’ada ta tanadar ko da kuwa ya fito ya yi shawagi a kan dawakai da sunan hawa.

“Hawan Durbar kamar yadda al’ada ta tanada yana ƙunshe da wasu tsare-tsare da ka’idoji.

“Ba zai yiwu ka yi hawa ba idan ba ka zaune a Gidan Rumfa wanda a tarihi da kuma al’ada daga nan ake fitowa a soma hawa wanda ya samo asali daga Sarkin Kano Rumfa,” a cewar Kurawa.

Ado Kurawa ya bayyana yadda hawan sallah yake a ƙa’ida ta al’ada da ya ta’allaƙa da wasu matakai wanda yake farawa da fitowar Sarki a ranar Sallah daga Gidan Rumfa ta Ƙofar Fatalwa, sanye da fararen tufafi da farar alkyabba, sannan ya tafi Filin Idi, inda a yayin dawowarsa zai biyo ta wasu hanyoyi da su ma al’ada ta tanadar.

Saboda haka a cewar Kurawa, tun da Sarki Aminu ba a Gidan Rumfa yake ba a halin yanzu, ba shi da damar jagorantar hawan Sallar la’akari da cewa bai cika ƙa’idojin da al’adar Hawan Durbar ta tanada ba.

Kurawa ya kuma yi zargin cewa Aminu Ado na ci gaba da ɗaukar kansa a matsayin Sarkin Kano ne kawai saboda ya samu goyon bayan Gwamnatin Tarayya.

Aminiya ta ruwaito cewa tun a bara ake ci gaba da taƙaddama kan Masarautar Kano bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da Sarki Sanusi II karagarsa.

A halin yanzu dai Sarki Sanusi II na zaune a Gidan Rumfa yayin da Sarki Aminu ke zaune a Gidan Sarki na Nasarawa, kuma kowanne daga cikinsu na tutiyar cewa shi ne halastaccen Sarki a yayin da ake dakon hukuncin da kotu za ta yanke kan taƙaddamar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

An haramta hawan Sallah a Kano

Tuni dai ita kuwa rundunar ’yan sandan Kano ta haramta hawan sallah tana mai kafa hujja da dalilai na tsaro.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Juma’a.

CP Bakori ya ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan ƙaramar sallah da za a soma ranar Lahadi ko Litinin.

“Haka kuma an haramta duka nau’ikan hawan sallah da duk wata kilisa ta dawakai ko tseren mota a lokacin bukukuwan sallah ƙaramar da ke tafe,” in ji sanarwar.

’Yan sandan sun ce sun ɗauki matakin ne sakamakon rahotannin tsaro da suka samu da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al’ummar jihar.