An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana.
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya aminta da ganin jinjirin watan Shawwal a yau Asabar 29 ga watan Ramadan 1446 wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris 2025.
Sarkin Musulmi ya ce dangane da bayanan da suka samu na ganin wata a wurare daban-daban a Nijeriya daga Fadar Shehun Borno da Sarkin Zazzau da Ƙungiyar Izala mai hedikwata a Jos da sauran mutane don haka Azumin watan Ramadan ya zo ƙarshe daga yau Asabar.
Tun farko ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Aminiya ta ruwaito Mallam Simwal yana cewa ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi.
Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.