Tsohon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Abdulrahaman Kawu Sumaila, ya ce yi wa Kundin Tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima ne kadai zai kawo wa kasar mafita daga halin da take ciki a halin yanzu.
Sumaila, wanda shi ne dan takarar Sanatan Kano ta Kudu a jam’iyyar NNPP, ya bayyana hakan ne lokacin da ya zanta da manema labarai a Kano da safiyar Laraba.
- Majalisar Dokokin Kano ta bai wa Ganduje damar karbo bashin N10bn
- PDP ta fara tantance wanda zai tsaya a mata takarar Mataimakin Shugaban Kasa
A cewarsa, “Idan na zama dan Majalisar Dattawan Najeriya, zan dage wajen ganin an yi wa Kundin Tsarin Mulkin kasar nan cikakken nazari da kuma gyara.
“Kasa mai yawan al’umma kamar Najeriya mai dauke da mutane sama da miliyan 200 a ce tana da Babban Sufeton ‘Yan Sanda guda daya ko shakka babu dole za a fuskanci kalubalen tsaro,” cewar Kawu.
Kazalika, ya ce ya fuskanci akwai bukatar yi wa kundin kwaskwarima cikin gaggawa.
Har wa yau, ya ce akwai bukatar tsarin da zai taba rayuwar al’umma tun daga tushe, inda ya ce bai wa Kananan Hukumomi damar cin gashin kansu ita ce mafita.
A cewarsa akwai matsaloli da yawa da Kundin Tsarin Mulkin kasar nan ya haifar kamar rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da matsalolin zamantakewa, wanda ya ce akwai bukatar a sake duba shi ta yadda zai yi daidai da bukatun al’ummar kasar nan.