A wannan mako Aminiya ta tsakuro wani abu ne kan tarihin Kundin Mulkin Masarautar Kano inda muka tattaro wasu daga cikin binciken masana a kan tsarin mulkin masarautar wanda daya daga cikin Sarakunan Habe, Sarki Muhammadu Rumfa ya samar domin tafiyar da mulkin Birnin Kano:
Kudin Tsarin Mulkin Masarautar Kano, kundi ne da fitattaccen malamin Muslunci Muhammadu Mughili ya rubuta wa sarkin Kano Muhammadu Rumfa sama da shekara 400 da suka shuɗe.
Littafi ne da yake ɗauke da wasu ƙai’doji da dabaru da shawarwarin gudanar da sarauta da kuma muƙamai da sauran abubuwa da malamin ya rubata wa Sarkin domin ya samu cikakkiyar damar gudanar da mulkinsa a bisa tafarkin addinin Musulunci.
Wadansu jama’a da dama suna ganin cewa, wannan kundin tsarin mulki kusan shi ne maɓuɓɓugar dabarun gudanar da mulki a fakaice da Turawan Mulkin Mallaka suka yi amfani da shi da farko a Arewacin Najeriya, daga baya a duk faɗin Najeriya, daga ƙarshe kuma a duk ƙasashen da suka mulka a yankin Afirka ta Yamma.
Wazirin Kano Abubakar (1972), ya labarta cewa, a lokacin da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya hau karagar sarautar Kano, ya waiwaci tsare-tsare da kuma salon sarautar Hausawa domin samun cikakken goyon bayan Kanawa wajen gudanar da mulki. Kuma sannu a hankali waɗannan tsare-tsare su ake gani a cibiyar Daular Usmaniyya, kama-kama har lokacin da Turawa suka ci Ƙasar Hausa da yaƙi, suka fara tsarin Hukumar Gargajiya, sannan suka faɗaɗa sauran lardunan Arewa har zuwa dukkan ƙasashen da suka mulka a Afirka ta Yamma kamar yadda fitaccen masanin tarihin Afirka ta Yamma, Farfesa Boahen (1986), ya wallafa a Littafinsa.
Abin da ke cikin Kundin
Bayan haka, Allah Ya datar da kai da jin trosonSa, Ya tsare ka daga fizgar son zuciya. Haƙiƙa sarauta halifanci ne daga Allah sannan wakiltar Manzon Allah (SAW) ne. Yaya girman falalarta! Yaya nauyin maɗaukinta!
Idan Sarki ya yi adalci tsoron Allah zai yanka shi ta hanyar tsinke jijiyoyin son zuciya. Idan kuma ya yi zalunci son zuciya zai yanka shi ta hanyar tsinke jijiyoyin tsoron Allah.
Na gargaɗe ka da jin tsoron Allah “Kowane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijarorinku kawai ne a Ranar Ƙiyama. To, wanda aka shigar da shi Aljanna, to, lallai ne ya tsira. Kuma rayuwar duniya ba ta zama ba face jin daɗin ruɗi.” (Alƙur’ani:3:185).
Babi na Farko
Babi ne da ya yi magana a cikin kyautata niyya ga Sarki a cikin dukkan al’amuran sarautarsa. Cewa ya ƙudirci neman yardar Allah da wannan sarauta tasa ba duniya ba. Malam ya ce:
Dole ne a kan Sarki ya kyautata niyya a cikin sarauta. Ya nemi taimakon Allah a cikin dukkan al’amuransa. Ya ƙudirci samun yardar Allah da ita ta hanyar gyara al’amuran da suka shafi addini da duniya na bayin Allah.
Ya sani cewa, haƙiƙa Allah bai jiɓintar da shi a kansu domin kawai ya zama shugabansu ba, a’a, sai domin ya daidaita musu addininsu da duniyarsu. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.
Babi na Biyu
Daga cikin abubuwan da suke zama dole a kan Sarki (shugaba kowane iri) akwai kyautata kwarjininsa a majalisa ta hanyar bayyana son alheri da ma’abotansa da kuma ƙin sharri da ma’abotansa.
Cikin abin da ya shafi tufafi, to ya yi sutura da abin da yake halattacce ne ga maza (wato abin da aka sani na suturar maza), wanda bai yi kama da na mata ba. Kada ya ɓarnatar da dukiyar talakawa a wajen ado. Kada ya yi ado da zinare ko azurfa da kuma alharini.
Dole ya zauna a cikin natsuwa ba tare da wasa ba, kuma sannan kada ya zama mai ƙyalƙyala dariya. Ya zama mai runtse ganinsa, mai karɓar ra’ayi bisa gaskiya. Ya zama mai ƙin abubuwan ƙi irin su ƙarya, saɓa alƙawari da kuma gafala a cikin umarninsa da haninsa.
Mutanen da ke zagaye da shi su zama mutanen kirki ne da kuma malamai masu son alheri da masu tsoron Allah da masu gyara da masu gudun duniya. Duk su zama su za su kusance shi. Sannan ya nisanci jahilai da fajirai.
Ya zamo jajirtacce a cikin rarraba dukiyar al’umma da kuma tsare sarautarsa a kan kansa da kuma iyalansa. Kada ya zamo bawan riga (duk wanda ya ga dama ya ɗauka ya saka), kada kuma ya zama doki (kowa ya so, sai ya hau kansa) kuma kada ya zama shimfiɗa (kowa ya zo ya hau kanta ya huta) kuma kada ya zama wurin zama (duk shimfiɗar da ake so sai a shimfiɗa a kai a zauna). Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.
Babi na Uku
Babi ne da ya yi magana game da tsara masarauta ta hanyar rarraba ayyuka ga jami’an da za su dafa wa Sarki wajen gudanar da sarautarsa a dukkan faɗin masarautar. An lissafa muƙamai ashirin da biyar (25) daki-daki kuma kowane ɗaya da irin ayyukan da suka kama ce shi tare da siffofi ko siffar wanda ya kamata a naɗa a kan kowane muƙami. Malam ya ce:
Babi na huɗu cikin abubuwan da suka zama dole a kansa game da tsara masarautarsa ta yadda gyaranta zai zama abu mai yiwuwa a gare shi. Saboda zamowarsa mai kula da kowa sannan abin tambaya ne shi (a gaban Allah) game da su.
Wannan kuwa (kula da dukkan masarauta) ba abu ne mai yiwuwa a gare shi shi kaɗai ba, dole sai da wakilci. Saboda haka zai samar da muƙamai kamar haka:
Wazirai: Wazirai su ne masu taimaka masa a wajen kula da harkokin siyasa a dukkan faɗin masarautarsa (su ne irin su Galadima, Wali, Ciroma da sauransu). Su zamo marasa tsoron kowa sai Allah kaɗai.
Shugabanni: Su ne masu jagorantar garuruwan da suke nesa da shi. Masu tara masa jama’a a duk lokacin da yake buƙata (waɗannan su ne hakimai, digatai da masu unguwanni).
Alƙalai: Su ne masu raba rigingimu (wato masu gudanar da shari’o’i) a tsakanin jama’a. Su zamo masu tsoron Allah.
Jami’an tsaro: Su ne ’yan Hisba masu umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani ga aikata mummunan aiki. Masu kula da kai-kawon al’amuran birni da sauran abubuwan da suka shafi al’umma (kamar tarurrukan bukukuwa, ibada, zamantakewar ma’aurata da sauransu, abubuwan da suke buƙatar sasanci ba shari’a ba). Kuma masu gyara abin da ya lalace (na daga tarbiyya da sauransu).
Dogarawa: Su ne masu taimaka masa wajen kula da hukunce-hukunce (su ne masu kamo duk wanda ya yi laifi tare kuma da ladabtar da shi).
Fadawa: Su ne masu zama tare da Sarki; masu aiwatar da buƙatunsa domin kada ya buƙatu da wadansunsu.
Mashawarta: Su ne mutane masu hankali, waɗanda za su riƙa yi masa nuni a cikin abubuwa kafin abin ya kai ga jama’a (siffarsu ita ce hankali. Duk kuwa mutum mai hankali za a same shi da hangen nesa da taka-tsantsan da sauransu).
Ma’aikatan Zakka: Su amintattun mutane ne da za su riƙa karɓo dukiya suna sarrafa ta bisa dacewa (siffarsu ita ce amana).
Marubuta: Su ne waɗanda taskace dukkan abubuwa ya hau kansu.
’Yan aike: Su ne masu kai-kawo a tsakanin garuruwan Musulmi.
’Yan Leƙen Asiri: Su ne suke zama idon Sarki a garuruwan maƙiya (wato jami’an tsaron farin kaya ke nan).
Masu gadi: Su ne masu tsaron Sarki da rana. Masu tsaron Sarki da daddare.
Malamai: Mutane ne masu zuzzurfan sani ababen dogaro a fagen ilimi da kuma tsoron Allah. Aikinsu shi ne shiryar da Sarki a cikin dukkan lamuransa.
Masu ceto: Mutane ne da suke nema wa mai laifi rangwame game da horon da za a yi masa. Amma ban da waɗanda aka yanke wa haddi da kuma wanda ya ci haƙƙin wani (biyun ƙarshen nan dole a zartar da hukunci, babu sassauci).
Masu tsare-tsare: Su ne mutanen da suke yin gyara domin Allah.
Ma’aikatan Kuɗi: Su ne masu karɓo haƙƙin Allah kamar zakka da dukiyar ƙasa.
Ɗakin Ajiya: Ɗaki ne wadatacce wanda za a riƙa ajiye kayan abincin Sarki da abubuwan sha da sauransu.
Dawaki: A tanadi ƙarfafan dawaki a taskar dukiyar ƙasa domin hawan Sarki zuwa kai harin jihadi wasu biranen komai nisansu (daga cikin irin waɗannan dawaki akwai waɗanda ake tanada domin Sarki ya fice daga filin daga idan rana ta ɓaci. Saboda haka irin waɗannan dawaki akan same su da ƙarfi, gudu da kuma iya tsallake kwazazzabai da sauransu).
Guzuri: Dukiya ce da ake tanadarta musamman a taskar dukiyar ƙasa domin ɗawainiyar marasa hali a lokacin tafiya jihadi da sauran abubuwa.
Dakaru: Gwarazan mutane ne sannan kuma jarumai, waɗanda suke kewaye da Sarki a kowane lokaci domin shirin ko-ta-kwana.
Kayan yaƙi: A tanadi nagartattun kayan yaƙi irin su kwari da baka, masu, garkuwa, sulke da sauransu masu tarin yawa.
Likitoci: A samu mutane yardaddu, waɗanda za su riƙa bai wa mutane magunguna saboda kada su mutanen su buƙatu zuwa garin da ba nasu ba (kada su buƙatu da zuwa ƙasashen waje domin kiwon lafiya).
Shugabannin Rundunoni: Su ne mutanen da suke jagorantar rundunonin yaƙi (misali, Sarkin Baka da yake jagoratar maharba a filin yaƙi). Waɗannan su suke wakiltar Sarki a cikin lamarin yaƙi. Ayyukansu sun haɗa da shirya runduna, kare hasken Musulunci da sauransu.
Masana yaƙi: Mutane ne waɗanda ra’ayinsu yake yaye baƙin ciki, saboda tabbas shi yaƙi ɗan zamba ne, amma ba yawa ko sauri ba. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.
Munciro wani sashi na wannan rubutu daga littafib Kano ta Dabo Cigari na Wazirin Kano Abubakar A. Dokaji (1978). Kano, wallafar Northern Nigerian Publishing Company Limited. Zariya, Kaduna-Najeriya. Da kuma shafin intanet.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa