✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kulob din PSG ya kafa sabon tarihi a Faransa

A farkon makon nan ne kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa ya kafa sabon tarihi bayan ya lashe gasar rukunin kasar da…

A farkon makon nan ne kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa ya kafa sabon tarihi bayan ya lashe gasar rukunin kasar da aka fi sani da Ligue 1 ana saura wasanni takwas a kammala gasar.
Yin hakan ya sa kulob din ya shafe tarihin da kulob din Lyon ya kafa a shekarar 2007 bayan ya lashe gasar ana saura wasanni biyar a kammala.
Kulob din PSG ya kafa tarihi ne bayan ya lallasa kulob din Troyes da ci 9-0 a ranar Lahadin da ta wuce.
Shahararren dan kwallon  PSG Zlatan Ibrahimobic ne ya zura kwallaye hudu daga cikin tara da suka zura a raga.
Wannan shi ne karo na hudu da PSG take lashe wannan gasa a jere kuma karo na shida a jimulla. Yanzu kulob din ya ba na Monaco da ke biya da shi tazarar maki 25 yayin da saura wasanni 8 a kammala gasar.  Kenan ko da PSG ta rasa sauran wasannin da suka rage mata, kulob din Monaco ba zai iya kamo shi ba.