Kulob din Giwa FC da ke Jos a Jihar Filato ya ki bayyana a filin wasa da ke garin Ilorin a Jihar Kwara a wasan da zai buga da kulob din Wikki Tourist da ke Jihar Bauchi.
Idan ba a manta ba Hukumar da ke Kula da Gasar Firimiya ta kasa (LMC) ta dage kulob din Giwa wasanni uku na gida daga Jos zuwa Ilorin sakamakon kama kulob din da laifin cin zarafin alkalin wasa da tayar da husuma a lokacin da kulob din ya buga wasa da Enugu Rangers a makon wasa na 12 a garin Jos, inda aka dakatar da wasan a minti na 74 a lokacin da Rangers take cin 1-0.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ’yan kallo suka hallara a filin wasa na Ilorin don ganin yadda za a fafata tsakanin Giwa FC da Wikki Tourist, a karshe murna ta koma ciki bayan alkalin wasa Henry Ogunyanmodi daga Jihar Ondo ya dage batun wasan da misalin karfe 4:20, sakamakon rashin bayyanar Giwa, sannan ya bayyana cewa zai rubuta rahoton abin da ya faru.
Sai dai kocin kulob din Wikki Tourist Abdul Maikaba a lokacin da yake tattaunawa da ’yan jarida ya bukaci a ba shi maki 3 da kwallo 3 kamar yadda doka ta tanada idan kulob bai shiga filin wasa kasa da minti 15 da aka sanya lokacin fara wasan ba.
Duk da hatsaniyar da aka samu a Jos hukumar LMC ta sanya wata rana don a karasa wasa tsakanin Giwa da Rangers a Abuja, sai dai kulob din Giwa bai halarci wasan ba, al’amarin da ya sanya hukumar ta sanar da Rangers a matsayin kulob din da ya yi nasara a wasan bayan ta duba dokar hukumar ta B13.55 da ya ba ta damar bayyana Rangers a matsayin kulob din da ya lashe wasan.
Hakan ya sanya LMC ta ci tarar kulob din Naira dubu 200 da Naira dubu 650 don ba alkalan wasa da kuma Naira miliyan 1 don ba kulob din Rangers International.
Rashin bayyana kulob din a gaban kwamitin ladaftarwa na Hukumar LMC ta sanya ta ci kulob din tarar Naira miliyan 5.
Sanarwar da hukumar LMC ta fitar a shafinta na Intanet ya bayyana kamar haka: Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta gamsu da hukuncin da LMC ta yanke na bayyana Rangers a matsayin kulob din da ya samu nasara a wasa na 12 tsakanin Giwa da Rangers, sannan sakamakon rashin bayyana Giwa a gaban kwamitin ladaftarwa a yanzu an ci tarar kulob din Giwa Naira miliyan 5, sannan kulob din zai buga wasannin uku na gida a garin Ilorin da ke Jihar Kwara.”
An yanke wannan hukuncin ne sakamakon kama Giwa da laifukan da suka keta dokar hukumar ta B13.18 da B13.21 da B13.52 da C9 da C12 da kuma C1, “hakan ya sanya aka ci kulob din tarar Naira miliyan 5.”
Wata majiya da ke kusa da kulob din Giwa FC ta shaida wa Aminiya cewa wakilin Aminiya ne yake sanar da ita batun cin tarar da kuma dage kulob din wasanni 3 daga Jos zuwa garin Ilorin.
“A wurinka na fara ji, ni ban san da batun wata tara ko dage mu wasa zuwa garin Ilorin ba. Idan ka lura ga shi mun bayyana a filin wasa na Rwang Pam domin buga wasa da Wikki Tourist a nan Jos, amma abin mamaki ba mu gansu ba, sannan ga shi an kulle filin wasan, ga kuma jami’an tsaro.” Inji majiyar.
Majiyar ta kuma bayyana cewa kulob din Giwa mai bin doka da oda ne, domin ko a bara ma an dage kulob din wasa zuwa garin Kaduna, ya kuma buga wasa shida a can, amma a wannan karon kulob din bai san da wata tara ko dage shi wasa ba.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko yaushe wannan rikici zai zo karshe, domin dokar Hukumar LMC ta bayyana za a kori duk wani kulob da ya ki buga wasa 3 a jere ba tare da wani dalili ba, inda a yanzu Giwa bai buga wasan da aka shirya sake bugawa da Rangers da kuma wasa da Wikki Tourist ba.
Kulob din Giwa da Hukumar LMC sun sa zare
Kulob din Giwa FC da ke Jos a Jihar Filato ya ki bayyana a filin wasa da ke garin Ilorin a Jihar Kwara a wasan…