✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kullum sai na sha fitsarin shanu domin maganin COVID-19 —Akshay Kumar

Jarumin fina-finan Indiya na Bollywood Akshay Kumar ya ce yakan sha fitsarin saniya a kullum domin maganin COVID-19. Akshay Kumar na daga cikin dimbin mutanen…

Jarumin fina-finan Indiya na Bollywood Akshay Kumar ya ce yakan sha fitsarin saniya a kullum domin maganin COVID-19.

Akshay Kumar na daga cikin dimbin mutanen Indiya da ke da yakinin cewa fitsarin na maganin cutar.

Yana kuma daga cikin masu goyon bayan Jam’iyyar Firaminista Narendra Modi dan kabilar Hindu da suka ware miliyoyin Daloli don gano maganin cutar suga da cutar daji ta hanyar amfani da kashin shanu.

Har yanzu babu bayani a kimiyyance da ya tabbatar cewa kashi ko fitsarin shanu na dauke da sinadaran da za a yi magani da su, amma ‘yan siyasa masu goyon baya jam’iyyar Modi da ke mulkin kasar suna ikirarin suna maganin COVID-19.

Wasu ‘yan Indiya na shan fitsarin shanu

Jarumin dan shekara 53 ya jaddada abin da ya faru a wani fim da suka yi da Bear Grylls na gidan talbijin din kasar Iingila, inda suka sha shayi da aka yi da kashin giwa a gandun Indian Tiger Reserve.

“Jin dadin da nake yakan kore mani damuwa. Ina shan fitsarin shanu kullum dalilin ayurvedic.

“Saboda haka babu wata damuwa,” kamar yadda Kumar ya bayyana a tattaunawarsa da ya yi da wata kafar sada zumunta.