✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kullum kara kaunar Adam A. Zango nake yi —Safiya Chalawa

Auren Adam A. Zango da Safiya Chalawa a 2019 ya tayar da kura kan zargin shi da auri-saki

Safiya Chalawa, matar jarumi a Masana’antar Kannywood, Adam A. Zango, ta bayyana yadda kullum take kara son shi.

Safiya ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram, inda ta ce kulawar da yake nuna mata ne ya sa take kara son shi.

“Irin kulawar da kake nuna min a kullum take kara min tsananin kaunar ka. Ba zan taba mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili. Wato ranar aurenmu.

“Da a ce zan iya zama komai, da na zama ruwan hawaye a gare ka. A haife ni a idonka, na rayu a saman kumatunka. In mace a saman labbanka. Ina son ka, so mara misaltuwa.”

Idan ba a manta ba, a shekarar 2019 ce Adam A. Zango ya auri Safiya Chalawa, ya haifar da ce-ce-ku-ce kan zargin yana auri-saki.

Surutan sun taso ne ganin cewa ya auri mata da dama sun rabu kafin ita, wanda hakan ya sa ake tunanin ita ma ba za ta dade ba.

Kafin Safiya, Adamu ya auri mata biyar, amma duk sun rabu.

Amina ce matarsa ta farko kuma ita ce mahaifiyar dansa Haidar, sai Aisha ’yar Shika a Zariya wadda ta haifa masa ’ya’ya uku.

Matarsa ta uku ita ce Maryam daga Jihar Nasarawa, sai ta hudu Maryan AB Yola, wadda ta fito a fim din Nas.

Matarsa ta biyar ita ce Ummukulsum wadda ’yar kasar Kamaru ce, kuma ita ce ta haifi  ’yarsa Murjanatu.

Sai Safiya Chalawa, ta shida kuma ta haifa masa ’ya a bana.

%d bloggers like this: