Assalamu alaikum; barkanmu da sake haxuwa cikin wannan fili, da fatan Allah ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
A yau kuma in sha Allah ga bayani kan hanyoyin da ma’aurata za su yi amfani da su don samar da cikakkiyar kulawa da ingantacciyar tarbiyya ga yaransu a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan. Da fatan Allah ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu buqatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Koyar da su Azumi: Kamar yadda yake a bayyane cewa mafi yawan yaran Musulmi sun san ana azumi a cikin watan Ramadan duk shekara. Kuma da yawansu na dagewa wajen yin koyi da iyayensu da azumtar wani sashe na watan Ramadan.Haka kuma mafi yawansu ba su da cikakken ilimi game da azumi, ba su san me ya sa ake yinsa ba, ba su san amfaninsa ga rayuwa ba,ba su san darajojinsa ba. Don haka yana da kyau ma’aurata su ilimantar da yaransu game da watan azumi na Ramadan.Tun daga ma’anar sunan watan, tarihinsa, ayoyin Alqur’ani da suka yi bayani game da shi, matsayin ibadar azumi a cikin Musulunci, irin tarin lada, darajoji da rahamomi da Allah ya tanadar ma mai azumi da sauransu.
Bayan ma’aurata sun ilimintar da yaransu game da azumin watan Ramadana, daga nan kuma sai su koyar da su azumtar watan Ramadana a hankali har su saba.
Ma’aurata sai su bar zavin yin azumi gaba xaya a hannun yaransu; duk wanda ya ce zai iya a tashe shi ya yi sahur, in ya daure bai fasa ba a qyale ya kai abinsa har zuwa lokacin buxa baki. In kuma ya ce ya gaji zai ajiye, to sai a qyale shi, ya ajiye. Qananan yara waxanda ba su kai shekara goma ba sai a fara koya masu da yin rabin azumi, daga lokacin sahur zuwa sha biyun rana, manya kuma sai a riqa qarfafa masu gwiwa ta yadda za su riqa dagewa suna kai azuminsu ba tare da sun karya ba.
Haka kuma idan aka lura wani daga cikin yara ya galaibaita da azumi, ko xaukar azumin ya haifar da wata barazana ga lafiyar jikinsa, ko ba ya son ajewa sai a tilasta shi ya ajiye cikin lallashi da magana mai daxi.
Don gudun kada azumi ya galaibaitar da yara sosai, sai a tanadar masu abincin sahur mai xauke da dukkan sinadaran gina jiki, misali irin su wake, qwai, madara, alkama, da sauransu, haka nan ma abincin buxa baki. Sannan a koyar da su shan ruwa kaxan lokacin sahur ta yadda za su sha ruwa da yawa fiye da yadda za su sha in gaba xaya suka sha, wannan zai rage masu jin qishirwa sosai.
Haka kuma kada a bari su sha kayan zaqi irin su alewa da sauransu a lokacin sahur sai dai bayan sun yi buxa baki sai a ba su.
Sannan a riqa tambayar yaran da suka yi azumi irin abin da suke so a tanadar masu don buxa baki. Wannan kulawa ta musamman za ta sa su qara dagewa wajen yin azumin da rashin karyawa.
Yaron da aka lura yana son ya karya azumi ba tare da bayyanuwar wata galabaita a tare da shi ba, sai a lallashe kuma a yi qoqarin xauke masa hankali da kayan wasan yara kamar yadda aka ruwaito Sahabban Manzon Allah (SAW)na yi ma yaransu kwatankwacin haka lokacin da suke qoqarin koyar da su azumi.
Don qayatar da su da mantar da su yunwar da suke ji, ma’aurata na iya shirya ma yaransu abubuwan shaqatawa da za a riqa gabatarwa kullum da rana bayan sallar Azahar.Misali,ma’aurata na iya shirya ma yaransu wasan kacici-kacici a kan wani maudu’i na musamman wanda aka fahimci zai qayatar da su. Misali ma’aurata sai su zavi maudu’in azumin Ramadan, ko Sallah ko tarihin Annabi (SAW) da na Sahabbai da sauransu. Sai a shirya tambayoyi da amsoshin canka/zava game da shi, sai ma’aurata su raba yara zuwa gida biyu, uku ko yadda hali ya ba da, sai a riqa yi masu tambayoyi suna bayar da amsa, duk vangaren da ya ci sai a ba shi wata ‘yar kyauta, wannan zai sa xaya vangaren ma su qara dagewa don su ma ko sa dace da wannan kyautar.
Haka kuma ma’aurata na iya gabatar da wani wasa da ba ya buqatar kuzari da yawa don qayatar da yaransu a irin wannan lokaci.Misali, ana iya sa yara su zauna a qasa su yi da’ira, sannan uwargida ta naxa wani xankwali ko safa ta yi masa suffar qwallo; sannan sai a kunna ayoyin Al’qurani mai girma, misali a sanya daga Juz’in Amma a yo qasa.Sai suna miqa ma juna qwallon nan, kowane yaro sai ya miqa ma na kusa da shi cikin sauri kafin Surar da aka kunna ta kai qarshe; duk wanda wata Sura ta qare qwallo na hannunsa to ya fita wasan, sai sauran su ci gaba. Da haka har sai ya rage saura mutum xaya, wanda shi ya ci wasa ke nan.Sai kuma a samu wata ‘yar qaramar kyauta ta burgewa a ba shi don qara qayatar da abin. Sai dai a kula ba a surutu idan ana karatun alqur’ani don guje ma haka ana iya canzawa da wasu waqoqin Musulunci amma marasa kixa.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah ya sa mu dace da dukkan alheran da ke cikin wannan wata na Ramadan mai albarka, amin.