Masu garkuwa da mutane sun bullo da sabon salo na karbar kayan abinci bayan kudin fansa a hannun dangin mutanen da aka yi garkuwa da su a yankunan Abuja.
Dangogin wasu mutum 30 da aka sace a yankunan Kuje, Kwali, Gwagwalada da Abaji wata uku da suka wuce sun shaida wa Aminiya cewa baya ga kudin fansar da suka biya, sai da suka kai buhanan kayan abinci da kayan miya sannan aka sako ’yan uwan nasu.
- Yadda bakin ciki ya yi ajalin iyayen ’yan matan Chibok 17
- Ya kashe matarsa mai juna biyu a gadon asibiti
- Ban mutu ba, dogon suma na yi —Ummi Zee-zee
“Idan ba ka saya kayan ba, kudin kadai ka kai musu, to za su karbi kudin su ci gaba da rike dan uwanka sai ka kawo musu kayan abincin,” inji wani da aka yi garkuwa da dan uwansa.
Ya ce shi kansa, kudin fansar da suka bayar miliyan N1.5 sun kai wa masu garkuwar ne tare da buhun shinkafa biyu, da kwalin taliyar yara biyu da na sinadarin dandao kafin aka sako dan uwansa.
Bayan wani hari da aka yi garkuwa da mutane a Kiyi da Unguwar Hausa, ’yan bindigar sun shaida wa dangogin mutanen da suka sace cewa su kawo kudin fansa tare da buhunan shinkafa da kuma kjwalayen taliya da taliyar yara da kuma sinadarin dandano.
Iyalan wasu mutum takwas da aka yi garkuwa da su tare da limamin cocin RCCG da ke Kiyi, su ma sai da suka kai wa masu garkuwar kayan abinci da na miya.
Dan uwan wani daga cikin mutanen, ya ce dole ta sa ya sayo buhun shinkafa biyu da kwalayen taliya da na sinadarin dandano da sigari da giya ya kai wa ’yan da suka sace dan uwansa a kusa da Shenegu da ke Gwagwalada.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin mai magana da yawun Runduna ’Yan Sandan Abuja, a kan lamarin amma ba ta amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da ya aike mata ba, har muka kammala hada wannan rahoto.