An raba wa Gwamnatin Tarayya da jihohi kananan hukummomi Naira biliyan 696.965 na kudaden shiga da aka tara a watan Agustan shekarar 2021.
Bayanan kudaden da aka tara a watan na Agusta sun nuna an samu raguwar kudaden shiga daga bangaren mai da suka hada da harajin ribar man fetur da harajin ribar kamfanonin mai; haka ma harajin kamfanoni da kuma kudaden fito.
- Shehun Borno ya amince tsoffin ’yan Boko Haram su dawo cikin al’umma
- An kama dan sanda ya sato karafunan titin jirgin kasa
Majlaisar Rabon Kudade ta Kasa (FAAC) ta kara da cewa duk da haka harajin sayayyar kayayyaki (VAT) da na shigo da kaya daga kasashen waje sun karu sosai a watan Agusta idan aka kwatanta da abin da aka tara a watan Yuli.
Sanarwar bayan taron na ranar Laraba ta nuna daga cikin Naira biliyan 696.965 na kudaden shigar da matakan gwamnatin uku suka kasafta akwai harajin Naira biliyan 477.5 da hukumomin gwamnati suka tara da kuma harajin sayen kayayyaki (VAT) Naira biliyan 66.2.
An kuma tara Naira biliyan 50 daga bangare da ba na man fetur ba, an samu Naira biliyan 2.8 a matsayin ribar canjin kudade sai Naira miliyan 403 da aka kwato daga kudaden da bankuna ke cire wa kwastomominsu fiye da kima.
A kason da da kaa yi Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 289.3 daga cikin kudaden, sai jihohi Naira biliyan N217.183, sannan kananan hukumomi Naira 161.541.
Daga cikin kudaden shigar da aka raba, jihohi da ake hakar man fetur sun tashi da Naira biliyan 28.9 a matsayin kashi 13 daga cikin 100 na kudaden shiga daga bangaren man fetur da aka saba ware musu.