✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kudaden ‘Cryptocurrency’ na taimakawa ta’addanci – CBN

Babban Bankin Kasa na CBN ya ce yana nan a kan bakarsa ta haramta mu'amala da kudaden 'Cryptocurrency' na intanet, bisa zargin taimakawa 'yan ta'adda

Babban Bankin Kasa na CBN ya ce yana nan a kan bakarsa ta haramta mu’amala da kudaden ‘Cryptocurrency’ na intanet, bisa zargin taimakawa ‘yan ta’adda musayar kudi cikin sauki.

Bankin, a cikin wata sanarwa da mai rikon mukamin Daraktansa na Watsa Labarai, Osita Nwanisobi ya fitar ya ce sai dai haramcin har yanzu bai shafi halastattun hanyoyin musayar kudade ba.

Daraktan ya ce kasancewar hada-hadar kudaden na gudana ne karkashin kulawar wadanda ba su da izini ko lasisin harkokin kudi, dole CBN ya haramta kowacce irin mu’amala da su a Najeriya.

“Yin amfani da kudaden cryptocurrency tamkar yin karan-tsaye ne ga dokokin Najeriya.

“Sai dai yana da kyau a fahimci cewa akwai banbanci mai yawa tsakanin irin wadannan kudaden da kuma wadanda CBN ke bayarwa ta intanet.

“Kamar yadda sunansu ya nuna, namu CBN ne ke bayarwa, wadancan kuma wadanda suke bayarwa ba su da lasisi kuma babu mai kula ko sa ido a kan su.

“Wannan, na daga cikin dalilan da ya sa kudaden ke da saukin mu’amala wajen haramtattun ayyuka kamar zambar kudade, samarwa da ‘yan ta’adda kudade, cinikin makamai da kuma kaucewa biyan haraji

“Bankuna da dama da masu zuba jari da suka san mutuncinsu duka ba sa yarda su karbi kudaden saboda illarsu wajen aikata miyagun laifuka.

“Kowa ya san yadda ake amfani da irin wadannan kudaden wajen hada-hadar miyagun kwayoyi ta intanet. An kuma sami wasu rahotanni a kwanan nan wajen taimakawa ta’addanci, baya ga kawo nakasu ga halastattun hanyoyin musayar kudade,” inji Mista Osita.

A makon da ya gabata ne dai CBN ya sanar da haramta amfani da kudaden na Cryptocurrency a Najeriya tare da umartar bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade da su ma su yi haka ko su dandana kudarsu.