✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kuda wajen kwadayi akan mutu

A gobe miliyoyin ‘yan Najeriya za su yi dafifi a tashoshin jefa kuri’a da ke unguwanni ko kofar gidajensu don jefa kuri’a a zabubbuka uku…

A gobe miliyoyin ‘yan Najeriya za su yi dafifi a tashoshin jefa kuri’a da ke unguwanni ko kofar gidajensu don jefa kuri’a a zabubbuka uku da za a yi masu muhimamancin gaske, watau na shugaban kasa da kuma ‘yan Majalisar Dattijai da ta Wakilai da zai yi aiki tare da su. Shi ya sa wadannan zabubbuka da za a fara gudanarwa a karo na farko suka tsuma talaka, domin kuwa ya san ta kan su ne zai bi ya cire wa kansa kitse a wuta, bayan ya samar da shugaba da wakilan da za su tausaya masa, su kuma san da zamansa, su kuma yi rawa da bazarsa. To a nan ba wata magana, illa dai kawai a tunasar da talaka cewa soja fa malamin kansa ne, amma a fagen daga. 

Dalili kuwa shi ne ita dai gwamnati a ko ina take a duniya, walau wacce aka kafa ta ce da karfin tuwo ko wacce aka kirkiro bisa lalama da lumana, zaman talakawanta take yi, domin idan har ba su, to ita ma babu ita. Talakawa su ne tsaikon mulki, su ne suturar shugabanni, su ne kuma ke karkata akalar mulaka’u zuwa inda suke bukatar a nufa.
A lokacin mulkin jamhuriya ta farko abin da shugabanni da talakawansu suka sa a gaba shi ne kishin kasa da kuma girmama ra’ayoyin juna ta yadda za a fadi tare, a kuma tashi tare. Babu wani mai tunanin cewa me zai samu idan har ya sadaukar da kansa ga bautar kasarsa. Burin kowa shi ne kyautatawa mahukunta ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Wannan ne dalilin da ya sa mashahuran mazajen jiya suka bai wa talakawansu ingantaccen shugabanci, cike da adalci, rashin ha’inci ko zalunci da kuma karamci, suna masu girmama dukkan ra’ayoyin talakawansu da kuma aikata dukkan ababen da suka umurce su da aikatawa.
Amma su mazajen yau fa, mene ne manufar mulkin dimokuradiyya a wajensu, kuma ta wace sigar suke kallonta? Ai idan sun hanga, suka gano cewa babu abin da za su fitar ko su kankara don amfanin kansu, to ba makawa su da dimokuradiyya za su yi hannun riga. ‘Yan siyasar yau ba su da wata akida ko dimokuradiyyar da ta wuce ta kudi, idan kana da su kai ne mai farin jini, idan kuwa haka kake kwana aljihu ba ko karfanfana, ka kuma tashi hannu rabbana, to komai dadin bakinka, da dabarun jawo hankalin jama’arka, ba za ka yi wani tasiri ba a fagen siyasa komai ka yi sai a yi ta ganin wallenka.
Haka nan ma idan ka kasance mai tsananin kamanta gaskiya ko yawan fadinta za ka yi bakin jini a fagen siyasa. Shi yasa ma ‘yan siyasar suke shaguben cewa cikin da ke da gaskiya bai koshi. Watau ke nan ka ga sun halasta karya, domin ita ce cimarsu, kudi kuma dagutun bautarsu.
Dimokuradiyyar kudi da aka yi a jamhuriya ta biyu ta jawowa kasar nan gagarumar matsala domin shugabannin da suka yi ciniki da talakawa kafin zabensu, sun dukufa ne ka’in da na’in wajen farke dukiyar da suka narkar wajen zabensu tun da sanyin safiya. Bayan sun farke kuma sai suka dukufa wajen cika aljihunsu da na ‘ya’yansu. Mun dai ga yadda gwamnatin mulkin soja lokacin Janar Muhammadu Buhari ta takura wadannan zababbun shugabannin da kuma ‘yan kasuwar da suka kasance ‘yan kanzaginsu, har sai da suka amayar da dukiyar talakawan da suka hambuda.
A duk lokacin da aka yi amfani da kudi a fagen siyasa talaka ne za a kai a baro, domin da zarar an mika masa ‘yar wazobiya, da sandan sabulu, ko mudun gishiri da turmin namuzu, an toshe bakinsa ke nan. Yana ji yana gani za a yi dumu-dumu da dukiyarsa, ba dama ya hana, da karfi da yaji za a bata ‘yarsa, ba bakin magana, ko kuma a wawushe magungunan asibiti a dai-dai lokacin da yake gargarar mutuwa, ba halin hanawa. Ba mai damuwa idan ‘ya’yan talakawan da aka toshe bakunansu sun kasa zuwa makarantu, ko samun aikin da za a biya su duk wata. Hakanan idan matar talaka ta haihu, shi za a bari da biyan ungozoma domin dawainiyarta.
To yanzu kowa a kasar nan ya fahimci cewa da kudi ake neman kudi, saboda haka ‘yan kasuwa ma sun dukufa zubin adashi wajen ‘yan siyasa, domin sun fahimci cewa ana kafa gwamnati su ne kwasar farko, ta biyu ma su ne, haka ma su ne a kwasa ta uku, talaka kuwa ba ranar da za a ce shi ne ke da kwasa.
Su ma shugabannin siyasan yanzu sun gane cewa ashe dai da ma can bata lokacinsu suke yi zuwa kasashen ketare neman masu zuba jari, ashe akwai masu zubawa a nan cikin gida, sun baro su a baya. Saboda haka da shugabannin siyasa da hamshakan ‘yan kasuwa sun kulla abota don sayar da hannayen jarin rumbun talakawa, kuma wanda ya kasa awalaja mafi tsoka shi za a sallamawa.
‘KinjaAllaye’, in ji Babarbare, ashe dai yayin da wasu ‘yan siyasa ke murnar cewa za su mayar da kudi gida a sabili da ganin da suke sun sayi nagari, ladan kuturu kawai ne suka ci, bayan sun nemi makwadaitan ‘yan kasuwa su zo, su zuba masu jari. A nan sai mu yi fatan kada Allah ya sa idan ranar askin ta zo kazamin kuturu ne zai zauna dirshan a gabansu, su yi masa saisaye da gyaran fuska. Yanzu dai dabara ta rage wa mai shiga rijiya, ga zabe ya zo, ga ‘yan siyasa sun taho da buhunhunan kudi, to kada talaka ya yarda ya zama tamkar kudan da kan mace a fagen kwadayi.