Huduba ta biyu
Godiya ta tabbata ga Ubangjin talikai. Mai rahama Mai jin kai. Mai nuna Mulkin Ranar Sakamako. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne, kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da aminci mai yawa.
Bayan haka, ya ku Musulmi! Mafi girman abin da za a roki Ubangiji Madaukaki, shi ne a roki taimako kan samun yardarSa, shi ne abin da Annabi (SAW) ya koyar da masoyinsa Mu’azu bn Jabal (Allah Ya yarda da shi), inda ya ce masa: “Ya Mu’azu! Lallai ne ni, wallahi ina sonka, don haka kada ka manta ka rika fadi a karshen kowace Sallah; “Allahumma a’ini ala zikrika, wa shukrika wa husni ibadatika.” Ma’ana: “Ya Ubangiji! Ka taimake ni a bisa ambatonKa da yi maKa shukura da kyautata bautarKa.” Ibn Taimiyya ya ce, “Na yi nazarin mafi amfanin addu’a, sai na ga wannan addu’a ce da bawa ke rokon Ubangijinsa Ya taimake shi kan neman yardarSa, kuma na gan ta a Surar Fatiha cikin fadinSa: “Iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in.”
Ya ku taron Musulmi! Akwai muhimmin abin lura game da addu’a da nake ganin yana da kyau mu fadakar da juna a kai a nan wurin: Yana da kyau bawa Musulmi ya fahimci cewa, karbar addu’ar bawa daga Allah ba ta zama koyaushe, ko saboda girman mai addu’ar. Hakika bawa yana iya rokon Ubangijinsa wani abu kan Ya biya masa bukata, alhali a cikin abin akwai halakarwa da tabewa gare shi, sai ya zamo biyan bukatar za ta wulakanta bawan a idon Ubangiji, girmansa ya ragu, don haka sai Allah Ya ki amsa masa, saboda girmansa a wurinSa da son da Allah Yake yi masa, sai hanin ya zame masa garkuwa da kare mutunci, ba wai don Allah Ya yi masa rowa ba. To amma jahili, idan ya roki Allah, bai amsa masa ba, sai ya dauka Allah ba Ya son sa ne, ko ba Ya girmama shi. Ya rika ganin Allah Yana biya wa wasu bukatu, amma ban da shi, sai ya munana zato ga Allah. Shin ba Iblis ne Allah Ya fi ki a cikin halittarsa ba? Amma duk da haka, Iblis din ya roke Shi, kuma Allah Ya biya masa bukata. Amma da yake ba ta zama a bisa yardar Allah ba, sai ta kasance masa kari wajen tabewa da dada nesantar Allah da kore shi daga rahamarSa?
Don haka, ka sani, bayarwa da kin bayarwa daga Allah jarrabawa ce. Allah Ya ce: “To amma mutum idan Ubangijinsa Ya jarraba shi, wato Ya girmama shi, kuma Ya yi masa ni’ima, sai ya ce, “Ubangijina Ya girmama ni!” Kuma idan Ya jarraba shi, wato ya kuntata masa abincinsa, sai ya ce, “Ubangijina Ya wulakanta ni!” A’aha ba haka ba ne…” (k:89:15-17). Don haka samun sa’ada a duniya tana komawa ne ga “Iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in.”
Ya bayin Allah! Kuna sane cewa Musulmi yakan karanta “Ihdina siradal mustakim.” A kowace raka’a, domin ya jaddada bukatarsa ga Majibincinsa ta Ya shiryar da shi. To neman shiriyar ya kunshi shiriya daga Wanda Yake da iko a kanta, kuma take hannunSa, wato Allah, idan Ya so Ya ba bawanSa, idan Ya so Ya hana. “Kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa.” (k:18:49). Kamar haka, neman shiriya a ayar na nufin neman shiriya ga aikata ayyukan kwarai da dacewa da su bisa sauna da tsoro, tare da barranta daga tafarkin Yahudu, wadanda aka yi fushi da su, wadanda sun san gaskiya, amma suka yi girman kai, ba su yi aiki da ita ba, kuma da barranta daga tafarkin Nasara, batattu, wadanda suka bace nesa da gaskiya da shiriya, saboda bidi’o’insu, da Allah bai shar’anta musu ba. Malamanmu sun ce: “Duk malami ko masanin da bai yi aiki da gaskiya ba, to yana da wani yanki na kama da Yahudu, kamar yadda duk wanda ya yi aiki da son ransa, ko bidi’a a addini, yake da wani yanki na kama da Nasara.”
Bayin Allah! Ba domin bukatar Musulmi ta yau da kullum ba, ba don tsananin bukatarsa ga shiriya da kuma abin da ya bijiro wa Yahudu da Nasara na iya aukuwa da shi ba, ba domin wannan babban hadari da ke iya ruguza shi ba, da Allah bai farlanta masa yawan yin wannan addu’a ba. Amma sai Allah Majibinsa, Ya zaba masa ya rika kaskantar da kai gare Shi, a kowace rana da yin wannan addu’a akalla sau goma sha bakwai a wuni.
Don haka, babu abin da ya fi dacewa ga Musulmi, musamman a wannan lokaci, illa mu nazarci wannan sura mu fahimci ma’anarta.
Hakika kafirai sun bude fikokinsu, sun bayyana niyyarsu na murkushe da’awar Musulunci da kange ta da tuttuge ta daga tushe. Hatta bangarorin bayar da agaji na Musulunci ba su kubuta daga sharrinsu ba a ko’ina a duniya. Kafiran duniya sun nuna karara ba su tare da Musulmi, kuma Musulmi abokan gabansu ne. Duniya ta hadu don ganin bayan masu da’awa zuwa ga addinin Musulunci, duniya ta hada kai don kaskantar da Musulmi da wulakanta su, har suna rurrufe duk wata alama ta addini. Yahudu da Nasara sun dunkule, Yahudawa sun hade da Majusawa da masu bautar gumaka don ganin bayan Musulmi! Munafukai sun hade wuri guda a ko’ina tare da wadancan makiya don darkake Musulmi! An wayi gari haramun ne ka soki masu mamayar kasar Musulmi, ko ka taimaka wa masu yakin kwatar kansu da aka yi musu mamaya! Duk wanda ya yi haka, shi ne mujirimi abin kora!
Wannan shi ne taron dangin da Musulmi ba su taba gani ba. Domin a baya suna ta’addanci ne ga wasu, su kyale wasu, su kai hari wa wancan kasa ko gari, su kyautata wa wannan. Amma yau, sun game baki, sun hade kai domin yaki da kangewa da toshe hanyar isar kudade a tsakanin Musulmi ta kowace kafa da hanya! “Shin suna yi wa juna wasiyya da shi ne? A’a su dai mutane ne masu girman kai.” (k:51:53).
Kuma duk da irin wannan kaidi da makaru da saboda muninsu suka yi kusa su gusar da duwatsu, kada ka yi rauni ya kai Musulmi! Kada tarin makamansu su razana ka, domin ba wani karfi na hakika suke da shi ba, saboda sun kauce wa hanya madaidaiciya, karfi ne da karfin Allah Ma’abucin karfi zai wargaza shi. karfi ne da ba zai je ko’ina ba, saboda Allah Yana tsare addininSa a kullum. “Kuma mugun shirin kafirai, bai zama ba face a cikin bata.” (k:40:25).
Yanzu na san ka fahimci dalilin da ya sa aka ce ka barranta daga hanyarsu sau goma sha bakwai a kullum cikin fadinSa: “Ihdina siradal mustakim. Siradal lazina an amta alaihim. Gairil magdubi alihim walad dalin.”
Mafi rinjayen Malaman Tafsiri, sun ta fi a kan “magdubi alaihim” su ne Yahudu, “daluna” kuma su ne Nasara. Kuma hakika Hadisi ya zo da ke tabbatar da wannan daga Annabi (SAW), daga Hadisin Adiy bn Hatim (Allah Ya yarda da shi) kan kissar Musuluntarsa, ya ce: “Na tambayi Manzon Allah (SAW), game da fadin Allah Madaukaki “Gairil magdubi alaihim,” sai ya ce su ne “Yahudu” “Walad dalina” sai ya ce “Nasara su ne batattu.” Ibn Kasir (Rahimahullahu) ya ce, “Dukkansu, Yahudu da Nasara batattu ne da aka yi fushi da su, sai dai siffar da Yahudu suka fi kebanta da ita, ita ce ta “fushi” kamar yadda Allah Ya ce a kansu: “Wanda Allah Ya la’ane shi, kuma Ya yi fushi da shi.” (k:5:60). Da fadinSa: “Kuma suka koma da wani fushi daga Allah…” (k:2:61) da kuma fadinSa: “Kuma Allah Ya yi fushi da su…” (k:48:6). Sannan Nasara sun fi kebanta da “dalal” (bata), kamar yadda Allah Ya ce: “Hakika sun bace a gabani, kuma suka batar da wasu masu yawa, kuma suka bace daga tsakar hanya.” (k:5:77).
Lallai kafirai makiya ne da har abada ba za su tausaya muku ba, kuma idan ba su samu abin da suke so ba, suka yi shiru, to, don wata maslaha ce tasu, amma da sun samu dama sai su gaggauta darkake Musulmi: “Lallai su idan suka kama ku, za su jefe ku, ko kuwa su mayar da ku a cikin addininsu, kuma ba za ku samu babban rabo ba, sa’an nan har abada.” (k:18:20). Allah Ya yi mana gafara ni da ku.