An yi kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da matsayin Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello a kan allurar rigakafin cutar COVID-19.
Gwamnan dai ya sha nuna tababarsa a kan cutar inda ya ce sam babu ita a jiharsa ta Kogi, kuma a makon nan ya ce ba zai amince a yi masa rigakafin ba.
- Abin da ya sa ’yan mata ke son auren mazan da suka manyanta
- Ba zan yarda a yi min rigakafin COVID-19 ba – Yahaya Bello
Sai dai wani babban jami’i a Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya Kafa Kan Yaki da Cutar wanda bai amince a ambaci sunansa ba saboda ba shi da izinin magana a kai ya ce bai kamata Gwamnan ya hana ’yan Najeriya karbar rigakafin ba.
A cewarsa, tuni daruruwan mutane a jihar ta Kogi suka nuna sha’awarsu ta hanyar yin rijista a shafin gwamnati suna bukatar a yi musu rigakafin, duk da ra’ayin Gwamnan nasu a kanta.
“Za mu gani in Gwamnan zai yi amfani da karfin tuwo ne wajen hana masu son rigakafin a jiharsa ko a wasu wuraren. Na san za ka amince da ni cewa za a dauki tsattsauran mataki in hakan ta faru,” inji jami’in.
Da wakilinmu ya tuntubi Babban Jami’i Mai Kula da Rigakafi na kwamitin, Dakta Mukhtar Muhammad ya ki yarda ya ce uffan kan kalaman Gwamnan a kan rigakafin da ma cutar baki daya.
Sai dai ya shaida masa cewa tuni Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo da ma wasu jiga-jigan gwamnati suka karbi allurar, yana mai cewa hakan kadai ya isa ya zama kwakkwaran dalilin da zai sa sauran ’yan kasa ma su amince da ita.
Da muka tuntubi wasu mazauna garin Lakwaja babban birnin jihar ta Kogi sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi a kan matsayin da Gwamna Yahaya Bello ya dauka.