Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kolo Kyari, ya ankarar da al’ummar kasar game da wasu ’yan damfara masu amfani da sunansa a dandalin sada zumunta na Facebook.
Mele Kyari ya yi wannan gargadi cikin wani sakon ankaraswa da ya wallafa kan shafinsa na Twitter a ranar Alhamis.
Ya sanar cewa akwai mazambata da suka bude shafuka akalla 25 a dandalin sada zumunta na Facebook da sunansa domin su damfari mutane.
- An haramta wa yara aikin karfi bayan mutuwan takwas a Kaduna
- Mahara sun harbe ’yan banga 17 a wata arangama
A dalilin haka Kyari ya ke kira ga daukacin al’ummar Najeriya masu bibiyar zaurukan sada zumunta da su yi hattara domin gudun fada wa hannun miyagu.
Ya ce shi tun a shekarar 2015 ya daina amfani da shafin sada zumunta na Facebook.