Shugaba Buhari ya bukaci ’yan bindiga da su sako daliban Jami’ar Greenfield da sauran ’yan Najeriya da ke hannunsu.
Buhari bayyana hakan ne a yayin bayyana farin ciki game da sako ragowar daliban Kwalejin Gandun Dajin Tarayya da ke Afaka, Jihar Kaduna da aka yi garkuwa da su.
- Buhari na biyan ’yan bindiga kudin fansa —Obasanjo
- Daliban Afaka 27 da aka sako sun isa Hedikwatar ’Yan sanda a Kaduna
- Yadda kin karbar mara lafiya a asibiti ya ta da kura
Ya taya iyayen daliban da abokan arzikinsu murnar ne jim kadan da sako daliban a ranar Laraba, bayan sun yi sama da wata biyu a hannun ’yan bindiga.
“Muna godiya ga wadanda suka taimaka, musamman hukumomin tsaro, Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, Gwamnatin Jihar Kaduna da ’yan Najeriya ta suka taimaka da addu’o’i,” inji sakon da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar.
Da yake kira ga hukumomin tsaro da su jajirce a bakin aikinsu, ’yan Najeriya kuma su fahimci sha’anin tsaro, Buhari ya nuna damuwa kan yadda ya ce ake siyasantar da al’amarin tsaron kasar.
Shugaban ya sake jaddada shirin gwamantinsa na kare ’yan kasar ta yadda za su gudanar da harkokinsu ba tare da tsoron fadawa hannun ’yan bindiga ko masu garkuwa da mutane ba.