Shugabar Cibiyar Bincike Kan Harkar Lafiyar Abinci ta Kasa reshen jihar Ekiti, Misis Doyin Ajayi ya shawarci wadanda suka haura shekaru 50 a duniya da su guji ta’ammali da giya don kiyaye kamuwa da cututtuka.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ta bayyana hakan ne a Ado Ekiti, babban birnin jihar ta Ekiti a ranar Lahadi yayin da take zantawa da ’yan jarida.
- Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Kamaru 2 a Borno
- An cafke ’yan fashi da masu garkuwa da mutane uku a Adamawa
Ta shawarci wadanda suka kai wadannan shekarun da su fi mayar da hankulansu sha ’ya’yan itatuwa da sauran nau’ukan abinci mara nauyi.
A cewarta, shan giya a wadannan shekarun zai iya yin mummunar illa ga wasu sassa na jiki kuma ya haifar da saurin tsufa.
Misis Doyin ta kuma lura cewa masu shan giyar a kai a kai na iya lalata kodarsu, inda ta ce ko da shan giyar sama-sama shima ba shi da wata fa’ida.
Daga nan sai ta yi gargadi a kan cin nau’ukan abinci barkatai, tana mai shawartar jama’a da su rika tuntubar masana domin sanin irin abincin day a fi dacewa da su.