More Podcasts
Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma.
Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari
- NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan
Ɗaya daga cikin matsalolin da masana suka gano shi ne sare itatuwa ba tare da dasa sabbi ba, wanda ke illa ga muhalli.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazarin illar sare itatuwa ba tare da dasa wasu ba, da tasirinsa kan sauyin yanayi da kuma lafiyarmu.
Domin sauke shirin, latsa nan