Shugaba Buhari ya umarci Manyan Hafsoshin Tsaro da su tabbata sun kubutar da duk wani mutum da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da shi ba tare da bata lokaci ba.
Buhari ya ba da umarnin ne bayan zaman da ya jagoranci taron Majalisar Tsaro ta Kasa, inda shugabanin hukumomin tsaro suka yi mishi bayanin halin da ake ciki a bangaren tsaron Najeriya.
- Yadda Boko Haram ta yi wa mutum 11 yankan rago a Geidam
- Harin jirgin kasa: El-Rufai ya bai wa iyalan mutum 9 miliyan 18
Da yake jawabin bayan taron, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Babagana Monguno, ya ce shugabna kasar ya bayyana takaicinsa kan yawan asarar rayukan ’yan Najeriya da aka samu da kuma wadanda ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a baya-bayan nan.
Don haka ya umarci shugabannin hukumomin tsaron da na tara bayanai da su yi aiki tare wajen tabbatar da ganin babu ko mutum daya da ya rage a hannun ’yan ta’adda.
Umanrin nasa na zuwa ne bayan a kwanan bayan ’yan bindiga sun da wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna bom, suka kashe mutum tara daga cikin fasinjojinsa, suka jikkata wasu, sannan suka yi garkuwa da wasu da dama.
Monguno ya ce shugabannin tsaron sun gabatar wa Buhari rahotanninsu kan yadda ake kokarin yaki da matsalar tsaro, gami da shawarwarin matakan da ya kamata a dauka a matakai daban-daban har da kan iyakoki domin tabbatar da tsaron Najeriya.