Kotun Kolin Faransa ta amince da sabuwar dokar gwamnatin kasar da ta haramta wa mata Musulmi sanya hijabi ko abaya a manyan makarantu.
Kungiyoyin Musulmi na Action for the Rights of Muslim da Council of the Muslim Faith suka shigar da kara don kalubalantar dokar hana matan sanya hijabin.
- Za a yi kiɗan ƙwarya da na shantu yayin auren zawarawa a Kano – Daurawa
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Bambanta Sheikh Giro Argungu Sauran Malamai
Amma a yayin yanke hukuncin, kotun ta ce ba za ta iya amincewa da bukatarsu ba, kasancewar rufe jikin da mata ke yi ya saba wa dokokin da suka haramta nuna wata alamar addini a wuraren neman ilimi.
Kotun ta kara da cewa, ko a filayen wasanni ma, bai kamata mata su rika rufe jikinsu ba, kasancewar hakan na jefa fargaba a zukatan ’yan wasa da kuma hana sakin jiki.
Da ma tun ba yanzu ba hukumar kwallon kafar kasar ta haramta wa mata Musulami amfani da duk wani nau’in sutura da zai rufe jikinsu.
A cewarta, filayen wasanni ba wajen tallata addini, siyasa ko al’ada ba ne, waje ne na nuna ’yan uwantaka da son juna.
Sai dai tun wancan lokaci, kungiyar mata Musulumi ’yan kwallon kafa ta shigar da kara kuma har kawo yanzu kotu ba ta yanke hukunci ba.
Tuni dai wannan al’amari ya tayar da zazzafar muhawar tsakanin manyan ’yan siyasa a kasar.
Haka kuma, wata wallafa da Marine Lepen mai ra’ayin rikau ta yi na cewa “Dole ne mu hana hijabi a filayen wasa, za mu zartas da wannan doka kuma sai mun tabbatar ana biyayya gare ta” ta fara yawo a tsakanin jama’a a kasar.