Kotun Koli ta tabbatar da Ahmadu Fintiri na Jam’iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Adamawa.
A safiyar Laraba ne Mai Shari’a John okoro ya karanta hukuncin Kotun, wanda ya watsi da ƙarar ’yar takarar Jami’yyar APC, Aisha Dahiru Binani da ke ƙalubalantar nasarar Fintiri.
Kwamitin alkalai biyar na kotun d yake jagoranta ya bayyana cewa Kwamishinan Zaben INEC na jihar, Hudu Ari, ya aikata laifi wajen hana baturen zaben bayyana sakamakon zaben kamar yadda dokar zabe ta tabbatar.
Mai Shari’a John Okoro ya ce rashin barin baturen zaben ya bayyana sakamakon zaben, ya haifar da ruɗani.
- Yadda Takura A Wajen Aiki Ke Ta’azzara Rayuwar Ma’aikaci
- Sojoji sun kashe jagoran ’yan ta’adda sun ceto mutane 20 a Zamfara
Ya ce dokar zabe ta bayyana karara baturen zabe ne kaɗai yake da hakkin na sanar da sakamakon zabe.
Idan za a iya tunawa, a yayin da ake tsaka da tattara sakamakon zabe ne Hudu Ari ya sanar da cewa A’isha Binani ta lashe zaben.
Sanarwar daibta jawo ruɗani, kafin daga bisani INEC ta yi watsi da sanarwar ta umarci baturen zaben ya ci ga da aikin tattara sakamakon zaben da kuma bayyana wanda aya yi nasara a karshe.
Tun a lokacin INEC ta kira Hudu Ari domin ya amsa tambayoyi kan abin da ya aikata, kuma a halin yanzu yana ci gaba da fuskantar shari’a.
Bayan kammalawa ne baturen zaben ya sanar cewa Gwamna Ahmadu Fintiri ne ya yi nasara, domin yin wa’adin mulki na biyu.
Sakamakon haka Binani ta garzaya kotu tana neman a tabbatar da nasararta kamar yadda Hudu Ari ya sanar.