✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta kori dan takarar gwamnan APC na Taraba

Kotun Koli ta soke Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Taraba a Jam'iyyar APC

Kotun Koli ta soke Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar kujerar Gwamnan Jihar Taraba a Jam’iyyar APC.

A ranar Laraba lauyoyi biyar na Kotun Kolin, karkashin jagorancin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun suke soke dan takarar.

Gabanin haka, sai da Babbar Kotun Tarayya ta kori Sanata Bwacha bayan karar da David Sabo Kente, wanda ya nemi tsayawa takarar gwamna a Jam’iyyar APC ya sigar a watan Satumban 2022.

Kotun Kolin ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayyar bisa hujjar cewa haramtacce ne zaben dan takarar Gwamnan Taraba da APC ba ta gudanar, wanda ya samar da Bwacha.